Dembele zai shafe mako biyar yana jinya

Rahotanni daga kulob din FC Barcelona da ke kasar Sifen sun ce dan kwallon gaba a kulob din Ousmane Dembele ya ji rauni a cinyarsa ta hagu wanda hakan ya sa zai shafe kimanin mako biyar yana jinya ba tare da ya buga kwallo ba. Rahoton da kafar labarai ta Naij.com ta kalato ya ce […]

Dembele zai shafe mako biyar yana jinya

Ousmane Dembele

Rahotanni daga kulob din FC Barcelona da ke kasar Sifen sun ce dan kwallon gaba a kulob din Ousmane Dembele ya ji rauni a cinyarsa ta hagu wanda hakan ya sa zai shafe kimanin mako biyar yana jinya ba tare da ya buga kwallo ba.

Rahoton da kafar labarai ta Naij.com ta kalato ya ce Dembele ya ji raunin ne a wasan da suka yi da kulob din Athletico Bilbao a ranar Juma’ar da ta wuce kuma kulob din Bilbao ne ya samu nasara a wasan da ci daya mai ban haushi a gasar La-Liga ta Sifen.

Duk da yake dan kwallon ya yi wasa na tsawon minti 90, bayan an tashi wasan ne likitocin kulob din suka gano ya samu rauni a cinyarsa ta hagu kuma rahoton da suka fitar ya nuna zai yi jinya na mako 5 kafin ya koma fagen daga.

Dembele ya bi sahun Lionel Messi da Luis Suarez a ’yan kwallon da suka ji rauni a kulob din Barcelona.

A jibi Lahadi ne FC Barcelona za ta yi wasanta na biyu da kulob din Real Betis a gasar La-Liga ta da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya kamar yadda jadawalin gasar ya nuna.

A shekarar 2017 ce Dembele ya canja sheka daga kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus zuwa FC Barcelona na Sifen.