Diddigi: Gaskiyar lamarin Hakimi da matarsa

Kadarorinsa ne kawai ba za su shiga cikin wannan tsari ba.

Diddigi: Gaskiyar lamarin Hakimi da matarsa

A makon jiya ne aka samu labarin cewa matar dan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta PSG, Achraf Hakimi, mai suna Hiba Abouk ta bukaci ya ba ta rabin dukiyarsa a matsayin kudin ci gaba da kula da ’ya’yansu biyu da suka haifa, bayan ta nemi a raba aurensu.

Labarin ya tayar da kura matuka, inda har wadanda ba sa bibiyar harkokin wasannin kwallon kafa suka rika tofa albarkacin bakinsu.

Ba wannan ne karo na farko da aka samu irin haka a duniya, inda ko a fagen kwallo tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue sai da ya yi kusan tsiyacewa saboda mutuwar aurensa da matarsa Baturiya.

Sai dai a lamarin Hakimi, an ruwaito cewa dan wasan ba ya da dukiyar da zai ba matar, domin
dukiyarsa da kudin alawus dinsa mahaifiyarsa ake biya.

Aminiya ta bi diddigin lamarin, inda ta gano cewa manyan jaridun wasanni na duniya irin su Goal.com da Daily Mail da sauransu duk ba su kawo labarin ba.

Yadda lamarin ya faro

Aminiya ta gano cewa dan kwallon da matarsa, Hiba sun yi dauki makonni ba sa tare saboda tana zarginsa da neman mata.

Da take tabbatar da rabuwarsu, Hiba Abouk ta
rubuta a shafinta na Instagram cewa sun rabu kowa ya kama gaban kansa.

A cewarta, “Bayan shawara, ni da uban ’ya’yana mun yanke shawarar rabuwa.”

Sai dai duk da ta bayyana cewa ta shiga damuwa matuka bisa laifin da ya yi mata na ‘cin amana’, Aminiya ba ta ga inda jarumar ta ce tana neman mallakar rabin dukiyarsa ba.

Ana zargin dan kwallon da laifin fyade, wanda tuni ya bayyana a gaban kotu domin sauraron zargin da ake yi masa.

Hakimi da Hiba sun hadu ne a shekarar 2018, sannan suka yi aure a shekarar 2020.

Ke nan sun yi shekara uku ke nan yanzu, inda suke da ’ya’ya biyu.

Hiba jaruma ce, Musulma ’yar asalin kasar Tunisiya da aka haifa a kasar Spain kuma tana da shekara 36 a yanzu.

Sannan a watan Maris ne ta nemi a raba auren nasu.

Ta nemi a raba auren ne bayan an fara bincike kan zargin da ake yi wa dan kwallon na yin ‘fyade’ a gidansu na aure lokacin tana Dubai tana hutu da ’ya’yanta.

Hiba jaruma ce fitacciya a Spain, mai dukiyar gaske, wadda dama can da shahararta dan kwallon ya same ta.

Shi kuma Hakimi dan kasar Maroko ne, wanda yanzu haka yake taka leda a Kungiyar PSG da ke Faransa. Yana da shekara 24.

Hakimi fitaccen dan kwallo ne da ke dibar makudan kudi a kungiyarsa ta PSG, inda yake cikin zaratan ’yan wasa da duniyar kwallon ke yayinsu a yanzu.

Da yake martani kan lamarin, fitaccen mai sharhi wasannin da gabatar da shirin wasanni na Rediyon Freedom, Mohammed Suleman Mowiz ya ce labarin cewa duk dukiyar Hakimi mallakar mahaifiyarsa ce akwai rudu a ciki.

A cewarsa, “Ku yi watsi da duk wani labari da kuka gani cewa Hakimi ya yaudari matarsa ta hanyar mallaka wa mahaifiyarsa dukiyarsa.

Idan har ta tabbata cewa kotun ta yanke ya biya ta kudaden kula da yaransu, dole ne zai biya ta saboda suna da ’ya’ya biyu tare.

Ya ce “A nan batun ’ya’yan ake yi. Tunda suna da ’ya’ya biyu, to, dole ne ya ba ta akalla kashi 25 da abin da yake samu.

“Ina tunanin kadarorinsa ne kawai ba za su shiga cikin wannan tsari ba, idan sunan mahaifiyarsa ne a jiki.”

Yaya gaskiyar lamarin yake?

Aminiya ta bi diddigin lamarin, inda ta gano cewa lallai Hiba da Hakimi sun rabu, sannan a al’ada irin ta kasashen Turai, idan aka rabu a kan ba mata rabin dukiyar miji domin kula da ’ya’yansu ko kuma macen ta ba mijin rabin da take samu ko kusa da rabi.

Binciken Aminiya ya gano cewa a dokokin kasar Spain, kotu na dora nauyin kula ne idan daya daga cikin ma’auratan ya fi daya dukiya kuma bambancinsu ya fito fili.

Misali shi ne idan daya ya bar aikinsa don kula da gida domin daya ya ci gaba da nemowa.

Kudin kula da ’ya’yan yana danganta ne, amma a mafi yawan lokaci yakan kama ne daga kashi 15 zuwa kashi 40 na abin da wanda zai rika biya yake samu.

Duba da wannan dokar ce ta sa wasu suke tunanin tunda ba ya da kudi, kuma ita attajira ce za ta ba shi daga cikin dukiyarta, wanda ba haka lamarin yake ba, kasancewar ana biyan kudin ne ga wanda yake kula da ’ya’ya.

Sai dai kuma kasancewar dukkansu Musulmi ne, masu bin addini, akwai yiwuwar watakila a samu bambanci a dokokin, duk da cewa ko a Musulunci dole zai ci gaba da dawainiya da ’ya’yan alhali suna wajenta.

Sai dai a iya binciken Aminiya, ba ta gano inda aka samu tabbacin cewa dukiyar Hakimi na wajen mahaifyarsa ba.

Sakin aure da suka fi cin kudi a duniya

Kasancewar labarin Hakimi ya tayar da kura, Aminiya ta tattaro wasu mata bakwai da suka fi samun kuxi a matsayin sallamar bayan rabuwa da mazansu.

Melinda Gates

Attajirin duniya, Bill Gates ya sallama wa matarsa, Melinda Dala biliyan 127 na dukiyarsa saboda sakinta da ya yi.

Rabuwar auren shekara 27 tsakanin Bill , mutum mafi arziki na hudu a duniya a lokacin- da Melinda ita ce wadda aka ba da dukiya mafi yawa don sallamar matar da ta rabu da mijinta a duniya.

Jeff Bezos – Dala biliyan 38

Kafin Bill da Melinda, mai Kamfanin Amazon, Jeff Bezos shi ne mutumin da ya fi ba da kudi mafi yawa ga matar da ya rabu da ita a duniya.

A lokacin rabuwar Jeff Bezos da matarsa, MacKenzie Scott da suka shekara 25 tare a 2019, ya ba ta Dala biliyan 38.

Yanzu MacKenzie ita ce ta uku a jerin mata mafiya dukiya a duniya, kuma kimar dukiyarta ta kai Dala biliyan 6.1, shi kuma Jeff shi ne mutum mafi yawan dukiya duniya a lokacin.

Rupert Murdoch – Dala biliyan 1.8

A 1999 attajirin nan mai kamfanin yada labarai, Rupert Murdoch, ya saki matarsa ta biyu, Anna Maria Mann bayan sun haifi ’ya’ya uku.

A lokacin, Rupert ya sallama wa Murdoch kadarorinsa na Dala biliyan 1.7 da kuma tsabar kudi Dala miliyan 110.

Chey Tae-won – Dala biliyan 1.6

Rabuwar auren Chey Tea-won da Roh Soh yeong da kafafen yada labarai suka yi wa lakabi da Sakin Karni ya ci Dala biliyan 1.6.

Dukiyar da Chey ya mallaka wa Roh (wadda ’yar tsohon Janar din soja ce), ta kai kashi 42.3% na jarin kamfaninsa na SK Holdings Co. Chey Tea-won shi ne Shugaban SK Group, wanda shi ne kamfani na uku mafi girma a kasar Koriya ta Kudu.

Tiger Woods – Dala miliyan 710

Fitaccen dan wasan kwallon Golf na duniya, Tiger Woods ya sallama kadarorin Dala miliyan 710 ga tsohuwar matarsa, Elin Nordegren bayan mutuwar aurensu.

Woods da Elin Nordegren sun rabu a 2010 bayan shekara shida suna tare ta kuma haifa masa ’ya’ya biyu.

Michael Jordan – Dala miliyan 168

Shahararen dan wasan kwallon kwando na duniya, Michael Jordan, ya sallama wa Juanita Vanoy, Dala miliyan 168 bayan rabuwar aurensu a 2006.

A lokacin, Juanita ta zama matar da ta samu dukiyar sallamar rabuwar aure mafi yawa a duniya.

Harrison Ford – Dala miliyan 118

A 2004 tauraron fina-finan Hollywood, Harrison Ford ya mallaka wa matarsa, marigayiya Melissa Mathison Dala miliyan 118 bayan sun rabu.

Harrison da Mellissa Mathison suna da ’ya’ya 2 mace da na miji kafin rabuwarsu.

Song Joong-ki da Song Hye-kyo – Dala miliyan 86.5

Rabuwar auren taurarin fitaccen fim din Descendants of the Sun, Song Joong-ki da Song Hye-kyo ’yan kasar Koriya ta Kudu na daga cikin wadanda suka fi daukar hankali a Asiya.

Duk da rabuwarsu, maimakon sallama mata kadarori, sun ci gaba da tarayya a mallakar dukiyar da kimarta ta kai Dala miliyan 86.5.