Didier Drogba ya koma Kanada
Shahararren dan kwallon Kwaddebuwa da kuma kulob din Chelsea na Ingila Didier Droga ya sanya wa wani kulob a Kanada hannu mai suna Montreal Impact. Yanzu abin da ya rage masa shi ne samun izinin shiga kasar don ya fara yi wa kulob din wasa kamar yadda kulob din ya sanar a kafar sada zumuntarsa […]
Shahararren dan kwallon Kwaddebuwa da kuma kulob din Chelsea na Ingila Didier Droga ya sanya wa wani kulob a Kanada hannu mai suna Montreal Impact. Yanzu abin da ya rage masa shi ne samun izinin shiga kasar don ya fara yi wa kulob din wasa kamar yadda kulob din ya sanar a kafar sada zumuntarsa na Twitter a ranar Litinin da ta wuce.
Shugaban kulob din ya bayyana farin cikinsa a kan nasarar samun Drogba a matsayin wanda zai buga musu kwallo inda ya yi maraba da hakan. “Wannan ita ce daya daga cikin ranakun da ba za mu taba mantawa da ita ba, don zuwan Drogba zai taimake mu ta kowace fuska.”
Drogba, dan kimanin shekara 37, da yawa sun dauka ya gama kwallonsa bayan ya bayyana cewa watakila ya yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana a kulob din Chelsea na Ingila, amma sai ga shi ya sake sabunta kwantaragi a wani kulob da ke Kanada.
Sai dai ba a bayyana kudin da kulob din ya saye Drogba ba, duk da yake ya koma ne a matsayin na kashin kansa, ma’ana kwantaraginsa da kulob din Chelsea ta kare. Sannan kulob din bai bayyana yawan albashin da zai rika ba dan kwallon ba.
Da wannan sanya hannu da dan kwallon ya yi, zai kasance daya daga cikin ’yan kwallon da suka fi tsufa amma har yanzu suna cin gajiyar kwallo.