Diego Simeone ya amince da tayin da Chelsea ta yi masa
Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin kulob din Atletico Madrid na Sifen Diego Simeone ya amince da tayin da kulob din Chelsea na Ingila ta yi masa na komawa kulob din a karshen kakar wasa ta bana. Rahoton ya ce kulob din ya amince ya rika biyan kocin zunzurutun Fam miliyan 9.28 kwatankwacin Yuro […]
Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin kulob din Atletico Madrid na Sifen Diego Simeone ya amince da tayin da kulob din Chelsea na Ingila ta yi masa na komawa kulob din a karshen kakar wasa ta bana.
Rahoton ya ce kulob din ya amince ya rika biyan kocin zunzurutun Fam miliyan 9.28 kwatankwacin Yuro miliyan 12 a duk shekara a matsayin albashi.
Rahoton ya nuna tuni kocin ya sanar da kulob din Atletico Madrid akan yunkurinsa na komawa Ingila don ya ci gaba da horarwa a kulob din Chelsea a karshen kakar wasa ta bana.
Kulob din Chelsea dai kawo yanzu ba shi da takamaiman koci tun bayan da ya raba gari da tsohon kocinsa Jose Mourinho a watan Disamban 2015.
Mai kulob din Chelsea Roman Abramobic ya yanke shawarar daukar Simeone ne bayan ya rasa Pep Guardiola wanda ya rattaba hannu ga kulob din Manchester City na Ingila.
Diego Simeone dai ya samu nasarar lashe kofin La-Liga da kofin Europa da kofin Super da kofin Copa del Rey da kuma kofin Supercopa a kulob din Atletico Madrid tun bayan komawarsa kulob din a shekarar 2011.  Ya karbi ragamar kulob din ne a wancan lokaci a wajen kocin Watford na Ingila na yanzu kuikue Sanchez Flores.