Diezani ta zame wa Jonathan karfen kafa

Rashawa dai ta gawurta a kasar nan, kuma bisa ga dukkan alamu ta gagari gwamnatoci da shugabanninsu. A kullum sai labarin wani abin kunya, kamar wawurar makudan dukiyar talakawa ko mundahanar da shugabanni ke tafkawa game da cin amanar talakawa sun cika kunnuwan jama’a, kuma babu abin da suka iya yi illa su yi tsaki, […]

Diezani ta zame wa Jonathan karfen kafa
Diezani ta zame wa Jonathan karfen kafa

Rashawa dai ta gawurta a kasar nan, kuma bisa ga dukkan alamu ta gagari gwamnatoci da shugabanninsu. A kullum sai labarin wani abin kunya, kamar wawurar makudan dukiyar talakawa ko mundahanar da shugabanni ke tafkawa game da cin amanar talakawa sun cika kunnuwan jama’a, kuma babu abin da suka iya yi illa su yi tsaki, ko su yi Allah-Ya-isa. Abin takaici game da haka shi ne tun ana satar dubban Naira, har aka kai ga daruruwan miliyoyi, yanzu dubban miliyoyin Daloli ake sacewa, ba wani haufi ko juyayin sakamakon da zai iya biyo baya. Baicin haka nan kuma son kai da alfasha a dukkan harkokin gudanar da mulki sun zame abin kwalliya, kuma jama’a sun saba da su, ba wani mai nuna kosawa ko damuwa game da haka.
Shugabanni kuma sun shantake, ba abin da ya dame su, muddin dai hakan ba zai girgide kujerunsu na mulki ba, ko ya ingije su daga bisansu. Idan har jifa ta wuce kansu, to ta fada kan mai-uwa-da-wabi, ba abin da zai dame su. Wannan ne dalilin da ya sa kasar ta kasance tamkar ba doka da oda, kowa na aikata masha’a son ransa, a karkashin shugabanni masu wayo irin na shaho, wadanda ke assasa  zalunci har suna  yin galaba kan mutanen kirki.
Abubuwa biyu ne suka janyo wadannan masifun: Na farko dai shi ne rashin dagewar shugabanni wajen hukunta wanda duk ya aikata ba daidai ba, ko shi dan wane ne, don hakan ya zama darasi ga saura. Na biyu kuma ba a kame wadanda suka zalunci talakawa don a tatse dukiyar da suka sata da [wadda] suka hadiya, kuma hakan ya sa shugabanni da manyan jami’an gwamnati sun zame tamkar gafiyoyi, duk sun tsere da na bakunansu. Wannan babban bala’i ne da ya hana kasarmu ci gaba, jama’ar cikinta kuma na ganin koshi muraran, amma suna kwanan yunwa. A sakamakon haka talauci ya baibaye talakawa, ba wani mai walawa sai babban macucin talakawa da kasurgumin barawon dukiyar jama’a. Talaka da zuriyarsa sun zamanto ’ya’yan bora, haka nan suke zaman hannu-baka-hannu-kwarya, sun zame asfala-safilin, watau kaskantattun kaskantattu. ’Ya’yan shugabanni kuma da na manyan jami’an gwamnati sun zamanto ’ya’yan mora, ko a ce duwatsun da ke cikin ruwa ba su san ana rana ba, su ake tarairaya kamar kwai, ana shagwaba su da dukiyar sata.
Wadannan munanan abubuwan na faruwa ne kuwa a daidai lokacin da Najeria ke bukatar makudan kudaden da suke sulalewa aljifan manyan barayin gwamnati a yunkurin da talakawanta ke yi don samar da kayayyakin inganta rayuwa da habaka tattalin arziki. To sai ga shi nan ana kuka da manyan ministocin gwamnatin Shugaba Jonathan, musamman matan cikinsu, wadanda suka zake wajen almubazzaranci da dubban miliyoyin Nairorin talakawa wajen shirya wa kawunansu jin dadin duniya da sharholiyar da ba ta misaltuwa. Daga ka ji wance ta  sayi motoci masu sulken da harsashi bai iya kurdawa ciki, na dubban miliyoyin Nairori, sai ka ji takwararta a wata ma’aikata ta lale wasu dubban miliyoyi don hayar jirgin saman garari saboda yawon ta-zubar a kasashen duniya ita da iyalinta.
Misis Diezani Allison-Madueke, ministar ma’aikatar albarkatun man fetur ta zame diyar kuka mai janyo wa uwarta jifa, domin kuwa tun hawanta mulki ake ta Allah-wadai, ba a taba cewa madalla da ayyukanta ba. Ita kanta kawai ta sani, ba ta kuma tunanin komai sai sharholiya da yadda za a batar da dukiyar jama’a a banza don biye son zuciyarta.
A zamaninta ne rashawa da cin hanci suka yi kamari a ma’aikatar mai; matatun mai da sauran ma’akatun hakar mai suka durkushe da siradansu; aka kuma dinga samun bayanin abubuwan kunya da rashin aminci da ke wakana tsakanin manyan jami’an ma’aikatar. Ana cikin haka ne, sai ga shi nan an yi zargin bacewar wasu makudan kudade har Dalar Amurka miliyan dubu ashirin daga asusun  hukumar mai ta NNPC, kuma majalsar kasa ta shiga bincike. Maimakon wani abin alheri ya biyo bayan haka, sai kawai aka wayi gari babu man fetur da na dizal har ma da kananzir a gidajen mai don sayar wa talakawa. Amma kuma duk da haka nan sai ga waccan ministar ta yage baki, ba kunya ko tsoron Allah, tana cewa wajibi ne a kara farashin albarkatun man fetur, ciki har da kananzir din da talakawa suka fi ta’allaka a kai.
To a yanzu kuma sai ga shi nan ’yan majalisar kasa sun dukufa wajen bin bahasin zargin kashe makudan dukiyar talakawa har Naira miliyan dubu goma, a cikin shekaru biyu,  don hayar wani jirgin sama na garari. Talakawa da yawa sun yi murna da haka, amma wasu cewa suke yi wai ‘aikin banza, harara a duhu’ ake yi, wanda ake yi dominsa ko gezau ba zai yi ba, balle ya dauki matakin hukunta ta yadda ya kamata.
Ya dai tabbata cewa tsananin kwadayin abin duniya da shugabanninmu ke nunawa  da kuma kawazuncinsu na dawwama bisa mulki ta hanyar amfani da dukiyar sata, su ne ummul-haba’isin tsumburewar tattalin arzikinmu  da kuma mawuyacin halin da kasarmu ta zurma ciki, kuma ba wanda ya damu, a gida da waje, balle ya kawo mata dauki. To muddin irin su Diezani na ci gaba da mike kafa bisa kujerar mulki, kuma ubangidansu na dagewa wajen daure masu gindi, to ba ta yadda za a iya yin  maganin rashawar da ta kai kasar nan yin kaurin suna a kasashen duniya. An dai gane cewa ta zame wa Shugaba Jonathan karfen kafa, don ba yadda zai yi da ita.