Diket Plang ya lashe kujerar Sanatan Filato ta Tsakiya
Diket Plang na jam’iyyar APC, ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 131,129.
Hukumar Zabe ta Kasa INEC, ta ayyana Honarabul Diket Plang, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Filato ta Tsakiya.
Da yake bayyana sakamakon zaben a yau Asabar a hedkwatar Mazavar da ke garin Pankshin, Baturen Zaben, Dokta Jima Lar ya bayyana cewa Honarabul Diket Plang na jam’iyyar ta APC, ya lashe zaben ne, bayan ya samu kuri’u 131,129.
- INEC ta hana ’yan jarida shiga cibiyar tattara sakamakon zabe a Adamawa
- Sojoji sun harbe barawon akwatin zabe a Kebbi
Ya ce Yohanna Gotom na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu, ya samu kuri’u 127,022 a yayin da Garba Paul na jam’iyyar LP da ya zo na uku, ya samu kuri’u 36,510.
A cewar Dokta Lar, a bisa tanadin Dokar Zabe, ya ayyana Honarabul Diket Plang na jam’iyyar APC a matsayin Zababben Sanatan Filato ta Tsakiya.