Dillalai sun yi ƙorafi kan arhar man dizel ɗinmu — Matatar Dangote
Dilallai sun yi ƙorafin cewa rage farashin man dizel da muka yi yana barazana ga kasuwancinsu.
Dillalan man fetur a Nijeriya sun yi ƙorafi kan rage farashin man dizel da Matatar Dangote ta yi zuwa Naira 900 kan kowace lita.
A ƙorafin da dillalan suka aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu, sun ce rage farashin da Matatar Dangote ta yi yana zama wata babbar illa ga kasuwancinsu.
- Hatsarin tirela ya ci rayuka 21 a hanyar Kaduna-Abuja
- Mutane 9 sun rasu a hatsarin A Daidaita Sahu da mota a Kano
Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote, Devakumar Edwin ne ya bayyana hakan a wata tattaunawar kai tsaye ta Twitter Spaces da Nairametrics ta shirya.
“Masu sayar da man fetur a Nijeriya sun rubuta wa shugaban ƙasa Bola Tinubu ƙorafin cewa rage farashin da matatar ta yi daga Naira 1,200 zuwa Naira 1,000 sannan a yanzu ya koma N900 kan kowace lita, yana barazana ga kasuwancinsu,” inji shi.
Edwin ya bayyana wasu daga cikin ƙalubalen da Matatar Dangote ke fuskanta da kuma tasirinta ga wadatar man fetur da farashin man a faɗin ƙasar.
A cewarsa, matatar man da ke yankin Free Zone a unguwar Lekki da ke Legas, da ƙyar da ke iya sayar da tankokin man dizel 29 a kowacce rana saboda ƙarancin dillali masu saye a nan cikin gida.
“Sakamakon rashin samun kasuwa da ƙarancin masu saye a nan cikin gida, matatar tana fitar da mafi yawan man dizel da na jiragen sama zuwa ƙetare,” in ji shi.
Edwin ya ce za a fitar da man Matatar Dangote zuwa ƙasashen waje idan kamfanin mai na Najeriya NNPC da sauran dillalan man fetur a ƙasar suka ƙi sayen nasu.
“Mun yi ta fitar da man jiragen sama, muna samar da kananzir, muna samar da dizel, amma a jiya muka fara aikin samar da man fetur.
“Abin da kawai ya rage mana a yanzu shi ne mu soma samar da sauran sunadarai na albarkatun man fetur.”