Dillalan kwayoyi za su dandana kudarsu a Bauchi – NDLEA

Sabon shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Bauchi, Alhaji Muhammed Malami Sakkwato ya ce dillalan da ke hada-hadar miyagun kwayoyi za su fara dandana kudarsu domin hukumar ta fito da wasu sababbin dabarun yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar. Alhaji Malami ya bayyana haka ne lokacin […]

Dillalan kwayoyi za su dandana kudarsu a Bauchi – NDLEA
Dillalan kwayoyi za su dandana kudarsu a Bauchi – NDLEA

Sabon shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Bauchi, Alhaji Muhammed Malami Sakkwato ya ce dillalan da ke hada-hadar miyagun kwayoyi za su fara dandana kudarsu domin hukumar ta fito da wasu sababbin dabarun yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Alhaji Malami ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a karshen makon jiya.
Alhaji Malami ya ce hukumar tana ci gaba da wayar da kan matasan Jihar Bauchi kan illolin da ke tare da shan miyagun kwayoyi a wannan lokaci na mulkin dimokuradiyya.
Ya kara da cewa da yawa daga cikin matasa sun hauka ce a Najeriya sakamakon yadda suke tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Daga bisani ya shawarci dillalan miyagun su fahimci cewa daga yanzu hukumar ba za ta zuba ido tana kallon wasu mutane ’yan tsiraru marasa kishin kasa, suna lalata tarbiyyar matasan jihar ta hanyar miyagun kwayoyi ba.