Dillalin Aminiya a Jos ya samu kyautar Keke-Napep

Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Trust da Aminiya ya ba dallalin da fi kowa sayar da jaridar Aminiya a garin Jos da ke Jihar Filato a shekarar 2014 kyautar Keke-Napep. Mista Simple Lucky Atagbolo ya samu kyautar Keke-Napep ne sakamakon sayar da kwafin jaridar Aminiya 1000 a kowane mako da yake yi.Da yake […]

Dillalin Aminiya a Jos ya samu kyautar Keke-Napep
Dillalin Aminiya a Jos ya samu kyautar Keke-Napep

Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Trust da Aminiya ya ba dallalin da fi kowa sayar da jaridar Aminiya a garin Jos da ke Jihar Filato a shekarar 2014 kyautar Keke-Napep.

Mista Simple Lucky Atagbolo ya samu kyautar Keke-Napep ne sakamakon sayar da kwafin jaridar Aminiya 1000 a kowane mako da yake yi.
Da yake mika wa dallalin makullin Keke Napep din a ranar Talata, Manajan Kamfanin jaridun Media Trust na shiyyar Arewa ta Tsakiya da ke garin Jos, Malam Isa Danjuma Oboni ya ce wannan nasara da wannan dillali ya samu, wani babban kalubale ne ga sauran dillalan jaridar Aminiya. Don haka ya yi kira a gare su a kan su kara kokari wajen sayar da jaridar don ganin sun samu irin wannan kyautar ko ma wacce ta fi ta.
Ya ce “Muna fata nan da shekara biyu za mu zo Jos don mun ba wani dillalin jaridar Aminiya kyautar mota sakamakon irin kokarin da ya yi wajen sayar da jaridar.”
Ya ba da tabbacin kamfanin Media Trust zai ci gaba da karfafa wa dillalan jaridun kamfanin gwiwa, ta hanyar ba su kyautattuka sakamakon kokarin da suke yi wajen sayar da jaridun kamfanin.
A nasa jawabin Mista Simple Lucky Atagbolo ya bayyana matukar farin cikinsa a kan kyautar Keke-Napep da kamfanin ya ba shi, inda ya yi alkawarin shekara mai zuwa zai rika sayar da kwafin jaridar Aminiya 1500 a kowane mako.