dimbin asarar Jihar Barno

A makon day a wuce Jaridar Dailytrust ta ruwaito asarar rayuka dubu 20 da dukiyar Naira tiriliyan guda da biliyan 900 da aka tafka a Jihar Barno sanadiyya harin kunar bakin wake na Boko Haram. An fitar da alkaluman kididdigar ne bayan da aka shawo kan kunar bakin wake tare da rahoton tantance yadda za […]

dimbin asarar Jihar Barno
dimbin asarar Jihar Barno

A makon day a wuce Jaridar Dailytrust ta ruwaito asarar rayuka dubu 20 da dukiyar Naira tiriliyan guda da biliyan 900 da aka tafka a Jihar Barno sanadiyya harin kunar bakin wake na Boko Haram. An fitar da alkaluman kididdigar ne bayan da aka shawo kan kunar bakin wake tare da rahoton tantance yadda za a sake tabbatar da zaman lafiya, karkashin shirin da jami’an Gwamnatin barno ke gudanarwa , al’amarin da jami’an Bankin Duniya suka yi nazarinsa, suka bayar da kiyasin kididdigar. Wannan dimbin asarar na nuni da alkaluman kiddigar dukiyar gwamnati da ta mutane masu zaman kan su da hare-haren kunar bakin wake ya lalata a kananan hukumomin jihar 27.
Al’amarin da ya tabbata karara a rahoton, shi ne, gidajen al’umma miliyan uku da dubu232 da 308 da ke fadin jihar, kimanin 956, 453 ko kashi 30 cikin 100 duk hare-haren kunar bakimn wake ya lalalata su. Mafi muni shi ne na karamar Hukumar Mobbar, inda daga cikin gidajen mutane dubu 150 da 585, an rusa dubu 101 da 85. A kananan hukumomin Abadam da Guzamala da Bama da Gwoza an tafka barna, inda fiye da kashi 80 cikin 100 na gidajen karamar Hukumar Bama an lalata su.
Kuma rahoton ya bayyana cewa, ajujuwa dubu biyar da 335 an lalata su a makarantun Firamare da Sakandare da manyan makarantu biyu. Asarar Bama tafi muni, inda aka lalata ajujuwa 519 a makarantu 92, yayin da a Gwoza ma al’amarin ya shafi ajujuwa 420 a makarantu 70. An lalata gine-ginen makarantu a kananan hukumomi 24 daga cikin 27. Sannan an lalata kananan cibiyoyin kula da lafiya da sha-ka-tafi 201 da manyan asibitoci. Boko Haram ya lalata wuraren samar da ruwa har dubu da 630. Manyan gine-ginen birane 665 da suka hada da ma’aikatu da gine-ginen kananan hukumomi da kurkuku da ofishin ’yan sanda da ofishin samar da wutar lantarki duk lalata shi, inda a da ake da tashoshi rarraba wutar lantarki 726 da ke da karfin  11Kb/415b da layukan rabon wutar da suka kai 415  zuwa 230 b.
Wuraren shakatawa da gandun dazuka da wuraren kiwo da ayyyukan shawo kabn kwararowar Hamada da rafuka da koguna da tafki duk ba a kyale su ba; ko dai an zuba musu guba, ko an dasa bama-bamai a kananabn hukumomi 16. Sannan akwai dabbobi dubu 470 da ko aka kasha su ko aka sace. Mafi yawa akan asarar dukiya da rayauka dubu 20 na ’yan Jihar Barno an halaka su ne, bnaya ga mafi yawan mutum miliyan biyu da yaki ya raba su da gidajen su, ga kuma wasu dubbai da suka smau mafaka a kasashen da ke makwaftaka da Jihar Barno.
Wadannan alkwaluman kididdiga da ke bayyanai karara sun isa su tabbatar wa duniya cewa, babban bala’in da boko haram ya haifar wa kasar nan hakikanin yadda lamarin yake. Tushen wannan rahoto dai shi ne, Bankin Duniya ya bukaci jihohin da musifar ta shafa su tattara bayanan asarar su, a bisa zayyanar tsarin da aka bayar, su aike da shi don tantancewa da tabbatarwa. Sannan an bukaci jihohin Yobe da Adamawa da Gombe da Bauchi da Taraba su aike da irin wadannan bayanai don jami’an Bankin Duniya su tantance su.
Duk da cewa sauran jihohin Arewa maso Gabas sun tafka dimbin asarar rayuwa da dukiyoyi, ba za a iya kwatanta asarar su da ta Jihar Barno ba, inda cibiyar Boko Haram ta samu gindin zama. Asarar rayukan ’ya’yan jiha mutum dubu 20 da dimbin wadanda suka jikkata, baya ga kadarorin da aka lalata, wadanda kimar kudin su ta kai Tiriliyoyin Naira babbar musifa ce da tarihi ba zai manta da ita ba. An mayar da hannun agogo baya a wannan kasa mai dimbin tarihi da bunkasar al’adu tsawon shekara dubu.
Wannan ya zama nauyi ne da ya rataya ga hukumomin duniya da su yunkuro wajen gyara da mayar da makwafin wannan asara da aka yi. Aiwatar da wannan aiki tallafa wa rayuwar al’umma ce, kuma fadakarwa ce ga masu ra’ayi na kashin kan su. Kowane kwararren masani da ke bayanin dalilan da suka haifar da rikicin Boko Haram ya ambaci fatara da jahilci, a matsayin jiga-jigan al’amuran da suka haifar da matsalar. Don haka wannan dama ce ga daukacin duniya ta kowa ya shigo don bayar da irin gudunmuwarsa ga wadanda ke tsananin neman taimako bayan an jikkata su a sanadiyyar harin kunar bakin wake, ta yadda za su murmure su dogara da kan su. Baya ga haka ma, wata dama ce ta bibiyar al’amuran ci gaban kasa don tabbatar da cewa batattun masu tada kayar baya a yankin da ke ikrarin tsattsaurar akidar Musulunci ba su sake samun gindin zama ba a yankin, ballanta su yi wa duniya mummunar illa.
Baya ga Bankin Duniya, muna rokon kasashen Yammacin Turai masu dcimbin arziki da suka hada da yankin Scandinabia (wato Denmark da Norway da sauransu) da suaran kasashen Larabawa masu arzikin man fetur, da abokan mu na yankin Asiya, musamman kasar Sin da Japan da Indiya da Indonesiya da Malesiya da Koriyoyi, su kawo dauki Jihar Barno a kowane fanni suka zaba. Yanzu ne lokacin da ya dace duniya ta kawo dauki.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54