Dimbin bashin da Ganduje ya bar wa Kano abin takaici ne —Abba Gida-Gida

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi wa Ganduje sakayya da gwargwadon abin da ya shuka.

Dimbin bashin da Ganduje ya bar wa Kano abin takaici ne —Abba Gida-Gida

Abba a lokacin karbar mulki a Fadar Gwamnatin Kano

Sabon Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koka game da yadda tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bar masa bashin da ya zarta Naira biliyan 241.

Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi ragamar mulki da kuma kunshin bayanan yadda Ganduje ya tafiyar da mulki a Fadar Gwamnatin Kano.

Abba ya bayyana cewa, “Wanann abin da tsohuwar gwamnati ta yi mana abin takaici ne na bar mana bashin da kai sama da Naira biliyan 241.

“Yanzu a ina za mu samu wadannan kudaden har mu biya?” a cewar Abba Kabir.

Abba Kabir Yusuf ya bayar da tabbacin zai duba yadda gwamnatin da gabata ta gudanar da mulkin da kuma daukar matakan da suka dace.

Aminiya ta ruwaito yadda Ganduje ya tafi halartar bikin rantsar da sabon Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu a Abuja, lamarin da ya sanya ya wakilta Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ya maye gurbinsa wajen mika mulkin.

“Na zaci tsohon Gwamna Ganduje zai tsaya da kansa ya mika mulki kamar yadda aka saba a nan Kano. A shekarar 1999 kamar yadda Aminu Kwatagora ya mika mulki ga Kwankwaso.

“A shekarar 2003 Kwankwaso kuma ya mika mulki ga Shekarau.

“Haka kuma Shekarau ya mika wa Kwankwaso mulki a Shekarar 2011, shi ma Kwankwaso ya mika wa Ganduje mulkin a shekarar 2015.

“Amma kuma ni me ya sa ba zai tsaya ya mika min mulki ba sai dai ya sa wakili ?, inji Abba Gida-Gida.

Gwamna Abba ya bayyana cewa abin da ya sa shi da jama’arsa ba su amsa gayyatar da Ganduje ya yi musu na karbar mulki a jiya Lahadi 28 ga watan Mayu shi ne, don guje wa duk wani abu da zai iya zama karan tsaye ga Kundin Tsarin Mulkin Kasa na 1999.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba wa al’ummar Jihar Kano tabbacin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin bai ba su kunya ba.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi wa Ganduje sakayya da gwargwadon abin da ya shuka.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS