Dimokuradiyya romon jaba: ga wari ga dadi

Lokacin da al’umma ke sa ran za su mori romon dimukradiyya, na irin arzikin da Allah Ya hore wa kasarsu, duk ganin an kwashe shekaru a karkashin mulkin sojoji da ake zargi da yin sama da fadi da almubazzaranci da kudin al’ummar kasa. An samu wasu da dama daga cikin manyan ’yan boko da ’yan […]

Dimokuradiyya romon jaba: ga wari ga dadi
Dimokuradiyya romon jaba: ga wari ga dadi

Lokacin da al’umma ke sa ran za su mori romon dimukradiyya, na irin arzikin da Allah Ya hore wa kasarsu, duk ganin an kwashe shekaru a karkashin mulkin sojoji da ake zargi da yin sama da fadi da almubazzaranci da kudin al’ummar kasa. An samu wasu da dama daga cikin manyan ’yan boko da ’yan siyasar kasar  nan, wadanda suka yi rubuce-rubuce a game da irin yadda sojoji ke gudanar da sha’anin mulkinsu, tare da nuna rashin gamsuwa da mulkin soja. Irin wadannan mayan sun zargi gwamnatocin sojan kasar  nan, da lalata kasa ta bangarori daban-daban, ciki kuwa a kwai:  Rashin fadar albarkacin baki da koya wa na bayansu yin rub da ciki a kan dukiyoyin al’ummar kasa, ga zargin kashe darajar kudin kasa a duniya; ga kuma zargin ciwo dimbin bashi,musamman na (Paris Club) da na bankin duniya.

Hatta cin hanci da karbar rashawa da halasta kudin haram, suna zargin cewa wai duk shugabannin mulkin soja ne suka yi sanadin faruwarsu a kasar  nan.

To ka ji, sai dai tun lokacin da kasar  nan ta koma tsari irin na dimokuradiyya, manyan ’yan boko da ’yan siyasa, mun daina jin duriyarsu, duk da irin wandakar da ’yan siyasa ke yi da kudin al’ummar kasa. Mun san cewa idan za ayi  magana ta gaskiya, sha’anin mulki a duniya baki daya ba na soja ne ba, hakkin al’ummar kasa ne ta zabi irin shigabannin da take son su jagorance ta, don magance mata irin matsalolin da suka addabe ta, kamar yadda muke gani a wasu kasashen duniya da suka ci gaba. Sai dai wannan tsari na dimokuradiyya bai dace da kasashenmu na Afirka ba. Dalili kuwa shi ne,bari mu dauki kasar mu ta Najeriya wadda a cikin ta aka haifemu, a kuma cikin ta muka girma.

A lokacin da mulkin kasar  ke hannun sojoji, babu irin abubuwan da a yau suka buwaye mu, sun kuma addabi al’ummar kasar  nan, ba kuma mai yi musu magani sai Allah. Duk lokacin da kasar  nan ta yi zabe, wa ya Allah sahihin zabe aka yi, wa ya Allah dauki- dora aka yi, ba a kwashe wa lafiya. Don haka ‘dimokuradiyya ta zama romon jaba: ga wari ga dadi.’

A jamhuriyar farko, an samar  wa kasar  nan shugabanni masu kamanta adalci, irin su Sa,Abubakar Tafawa Balewa da Dokta Nmamdi Azikiwe (Zik) da Cif Obafemi Awolowo da Sa.Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da dai ire-iren mutanan da suka tafiyar da gwamnatin wancan zamanin. Sai dai ko a wancan lokaci ba a kwashe lafiya ba, domin sai da su Janar Ironsi (mai ritaya) rsuka sa Arewa ta yi mummunar asarar da har yanzu ta kasa cike gurbinsu, inda aka salwantar da rayukan su Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.

Daga nan aka wargaza tafarkin dimokuradiyya. Bayan sojoji sun yi juyin mulki, sai kuma suka sake dawowa da wannan tsari na dimokuradiyya, saboda irin surutan da suke sha a wurin kasar  Birtaniya [Ingila], a nan ma an sake mika wa gwamnatin farar hula a karkashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari, ita ma ba a wanye lafiya ba. Kwatsam jama’a ba su yi aune ba, sai suka ji cewa an samu bullar wani malamin addinin Musulunci a Jihar kano, wato Maitasine, kuma asalinsa ba mutumin kasar  nan ba ne;  rahotannin sun nuna cewa jiga-jigan ’yan siyasa ne suka daure masa gindi, domin yana yi musu aiki, suna kuma samun biyan bukata. Bayan ’yan sanda da ’yan sandan kwantar da tarzoma,duk abun ya fi karfinsu sai da aka hada da jami’an soja kafin a karya lagon Maitatsine, ban da rigingimu nan da can da suka yi ta faruwa a lokacin, jamhuriya ta biyu a karkashin Shehu Shagarin, a nan ma ba karamar hasara ne Arewa ta tafka ba ,don kuwa kusan duk mabiya malam maitatsine ’ya ’yan jama’ar Arewa ne, su kuma aka yi ta kashewa ba ji, ba gani, duk a cikin ribar dimokuradiyya.

Ba a nan ta tsaya ba, don kuwa sai da aka samu wasu daga cikin sojojin mu na nan Arewa suka yi jagorancin tunkude Alhaji Shehu Shagari, aka kuma kai shi gidan yari na tsawon lokaci, daga nan kuma dimokuradiyya ta sake wargajewa. Sojoji sun ci gaba da rike kasar  har lokacin da aka yi angulu da kan zabo.

A  jamhuriya ta uku kuwa, nan ma wasu masu fada aji a kasar  suka yi ruwa da tsaki, suka je gidan yari suka dauko Janar Aremu Obasanjo, suka ce da ma laifin da ake zarginsa da aikatawa sun yafe masa, duk da cewa kundin tsarin mulki ya hana mutumin da ya yi zaman jarun yin wani mulki a kasar  nan in ba na gidansa ba ne, nan ma suka nuna cewa ai su ne tsarin mulkin, suka sa aka kankare waccan doka, suka kuma damka masa kasar  a matsayin shugaban kasa.  Shi ma da fara aikin nasa ya fara kakkarya manyan sojojin da Arewa ke sa ran za su kare mata martabarta, duk ya tattarasu ya yi musu ritaya, a nan ma bai gama mulkin ba, sai da aka samu wani mummunan rikici a Jihar Filato, ga Zaki biyan suka kashe jami’an sojoji, nan ma aka tara jama’ar garin a kasuwa aka bude musu wuta kan mai uwa da wabi.

Sai kuma a lokacin jamhuriya ta hudu a karkashin jagorancin marigayi Malam Ummaru Musa ’Yar ‘aduwa, a nan ma an samu bullar wata kungiya a Jihar Borno, wato Boko-Haram, a wani umarnin da marigayi ’Yar ‘aduwa ya bayar a lokacin da zai bar kasar  nan.

Shin ko a wannan dimokuradiyyar akwai kokarin da gwamnati ke yi na warware rikicin Boko Haram da ya taso daga Maiduguri.

A sakamakon rashin tsaro yanzu hatta ’yan fashi da makami sukan yi amfani da bom ko nakiya, domin tarwatsa bankuna da caji ofis din ’yan sanda, duk kuma da cewa kungiyar ta Boko-Haram ta Musulmi ce, an samu wasu da ba musulmi ba da kai hare-hare, musamman a majami’un kiristoci,[coci-coci], har ta kai ga a wasu lokutan da in an kai hari kan ’yan kungiyar ta Boko-Haram sukan fito su yi sanarwar cewa ba su ne suka aikata wannan hari ba. To ka ji. Don haka ake zargin gwamnati a kan wannan irin ta’addanci, ba kuma a cire tsammanin cewa duk irin wadannan hare-haren,  ana yi ne domin Musulunci da musulmi, duk inda aka ga Musulmi sai a ce ga ‘dan Boko-Haram ,’ ko ga ‘dan ta’adda, idan kuwa ba haka ba, ta yaya za a ce Jihar Barno aka samu kungiyar Boko-Haram, alhalin jama’ar wannan jiha suna daga gaba-gaba wajen yin riko da addinin Musulunci?

 

Kwamared Ibrahim Dattijo ya rubuto daga Jihar Kaduna,08055611999,[email protected].