Dimokuradiyyar Kongo ta kai wa ’yan tawayen Hutu hari a karo na farko
Dimokuradiyyar Kongo a karo na farko ta kaddamar da kai wa ’yan tawayen Hutu hari. An kai harin ne a ranar Talata bayan ministocin kasar sun bukaci a kai wa ’yan tawayen FDLR da ke kasar hari tun bayan da wa’adin wata daya da aka ba su don su mika makamansu ya cika.An bayyana bazuwar […]
Dimokuradiyyar Kongo a karo na farko ta kaddamar da kai wa ’yan tawayen Hutu hari.
An kai harin ne a ranar Talata bayan ministocin kasar sun bukaci a kai wa ’yan tawayen FDLR da ke kasar hari tun bayan da wa’adin wata daya da aka ba su don su mika makamansu ya cika.
An bayyana bazuwar ’yan tawayen a kasar ne ya haifar da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru 20 a kasar.
Idan ba a manta ba kasar Rwanda wadda kabilar Tutsi ke jagoranta, ta kai wa kasar Dimokuradiyyar Kongo mamaya sau biyu, inda ta bukaci a kwace makaman da suke hannun ’yan tawayen FDLR.
A makon jiya ne majalisar dinkin duniya ta janye sojojinta saboda zargin wadansu janar biyu da hannu wajen keta hakkin dan Adam a kasar.
Harin wanda aka kaddamar da shi a Kudancin Kibu mai nisan kilomita 10 daga iyakar kasar Burundi ya samu nasara, inji hukomomin sojar kasar.
Wata majiya da ke kusa da ’yan tawayen ta ce tuni ’yan tawayen suka janye daga yankin sakamakon samun labarin za a kawo musu hari.
Mai magana da yawun gwamnatin Dimokuradiyyar Kongo Lambert Mende ya tabbatar da sojojinsu ba su gamu da tirjiya daga ’yan tawayen ba.
“Mun kwace makamai 10.” Inji shi..
An zargi ’yan tawayen FDRL da hannu wajen kisan kare dangi a kasar Rwanda a shekarar 1994, inda aka kashe fiye da mutane dubu 800.