Dimokuradiyyar Najeriya na cikin hatsari — Bugaje
Tsohon dan majalisar, ya yi wannan kalami ne biyo bayan dakatar da Sanata Ningi da Majalisar Dattawa ta yi.
Shugaban Kungiyar Samar da Shugabanci Nagari a Arewa (AM2G) Dokta Usman Bugaje, ya ce dimokuradiyyar Najeriya na cikin mawuyacin hali.
A cewarsa, dimokuradiyyar Najeriya ba ta samar da irin ci gaban da al’ummar kasar nan ke tsammani ba.
- Shugaban ƙasar Vietnam Van Thuong ya yi murabus
- Kotu Ta Kori Karar Da Ke Son A Hana Zabe Ranar Asabar A Najeriya
Bugaje, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis.
Ya yi wannan kalami ne a wani martani na dakatar da Sanata Abdul Ningi da Majalisar Dokokin kasar nan ta yi, bayan ya zargi Sanatoci da yin cushen tiriliyan 3.7 a kasafin kudin bana.
Bugaje, ya ce dimokuradiyyar Najeriya ba ta haifar da abin da ake so musamman a kan matasa ba, wadanda ake burin su yi karatu domin zama wasu a gobe.
“A bayyane yake cewa dimokuradiyyarmu tana cikin mawuyacin hali. Dimokuradiyyarmu ba ta samar da ci gaban da ake bukata ba. Duba da irin majalisun dokokin da muke da su tabbas ba inda za mu je. Dimokuradiyyarmu tana jefa ’yan kasa cikin talauci, da yawan ‘yan kasar nan tsarin dimokuradiyyarmu ne ya jefa su cikin kangin talauci.
“Dimokradiyyarmu ta rasa dalilinta, kimarta na raguwa. Mutuncin dimokuradiyyarmu na sake yin kasa,” in ji shi.
Bugaje ya kara da cewa, akwai bukatar a gaggauta dawo darajar dimokuradiyyar kasar nan a zukatan ‘yan kasa.
Ya ce majalisa na da hannu wajen sama da fadi da dukiyar al’umma a kasafin kudi yayin da ‘yan Najeriya ke fama da talauci da rashin aikin yi da sauran matsaloli da suka yi wa kasar nan katutu.
A gefe guda kuma, ya soki Sanatocin Arewa kan rashin goyon bayan tsohon shugabansu Ningi da sakataren kungiyar, Kawu Sumaila.