Dinkin Sallah: Dalilan da teloli ke saba alkawari

Yadda mutane ke taimaka wa teloli wajen saba alkawarin dinkin Sallah

Dinkin Sallah: Dalilan da teloli ke saba alkawari

Wani tela ya bayyana dalilan da ke sanya teloli ba sa cika wa masu ba su dinki alkawari, musamman a lokacin Karamar Sallah.

Buhari Shu’aibu Muhammad da ke dinki a kasuwar New Market a garin Jos, hedikwatar Jihar Filato, ya ce rashin tsari ke sa teloli karbar dinkuna fiye da kima a lokacin azumi saboda yawan kawo dinkunan da ake yi a lokacin.

Da yake zantawa da Aminiya, Buhari ya ce, “Sau tari za ka ga telan da ya dade bai sami dinki ba, sai a irin wannan lokaci, za ka ga ana ta kawo mishi.

“Sau da yawa sai tela ya manta da irin dawainiyar da zai yi, kafin ya farga sai dinkunan da ya karba sa fi kirfinsa.

“Wannan dalili ne ya sa ake samun rashin cika, alkawari daga wajen teloli,” a zo ana rikici da su a cewarsa.

Jin kunya

Buhari tela, ya bayyana cewa bayan haka, “Masu kawo dinki, idan ka ce aiki ya yi maka yawa, ba za ka sami damar yi ba;

“Wani ba zai yarda ba, wani kuma za ka samu akwai kunya a tsakani; don haka sai tela ya ji nauyin kin karba.

“Amma kamar ni, idan mutum ya kawo mini dinki, na gwammace mu yi fada da shi, kan ban karbi dinkinsa ba, da na karba mu zo muna fada a kan ban yi mishi ba.”

Kawo dinki a makare

Buhari Shu’aibu ya yi bayanin cewa, “Halin da ake ciki a kasar nan ne ya sa masu dinki ba sa kawo dinki da wuri.

“Wani sai azumi ya zo karshe, sai Allah Ya kawo mishi wata hanya, ya samu ya sayi yadi ya kawo.

“Muna ganin wasu ba sa samun yadin ne da wuri, wasu kuma suna ta abinci ne, amma duk da haka wani idan ya samu kofa, sai ya je ya sayi yadi ya kawo.”

Rashin samun dinki

Ya ce dangane da masu kawo dinki ba su samu ba, wasu idan ba su sami dinkin ba, sukan yi hakuri.

“Wani duk abin da za ka gaya mishi ba zai yi hakuri ba, sai dai a yi ta musayar maganganu, har a kai ga samun sabani.”

‘Dalilan da nake cika alkawari’

Abdullahi Jafar wani tela ne shi ma a kasuwar ta New Market a garin Jos, ya bayyana cewa shi  ba ya samun matsala wajen cika wa mutane alkawari a dinkin da yake yi.

Don haka yana da jama’a da dama daga wurare daban-daban da suke kawo mishi dinki.

Ya ce, dalili shi ne duk wanda ya kawo mishi dinki, yakan fada mishi gaskiya idan ba zai sami damar yi ba.

Ya shawarci teloli, kan duk abin da mutum ba zai iya ba, ya fito ya fadi gaskiya.

“Abin da zai iya ya karba, abin da ya san ba zai iya ba, kada ya karba,” inji shi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos