Kogi: Dino Melaye ya bukaci a soke zaben kananan hukumomi 5
Dan takarar na jam’iyyar PDP ya bukaci sake gudanar da zaben a wasu kananan hukumomi biyar.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Kogi, Dino Melaye, ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke zaben wasu kananan hukumomi biyar na jihar.
Melaye ya yi zargin an yi magudi a kananan hukumomin Okene, Okehi, Ajaokuta, Adavi, da Ogori/Mangogo.
“Dole INEC ta soke zaben a kananan hukumomi biyar da ke mazabar Kogi-Tsakiya.
“Zaben Okene, Okehi, Ajaokuta, Adavi, da Ogori/Mangogo wata zamba ce da aka hada kai da ma’aikatan INEC,” in ji Dino Melaye ta shafinsa na X.
Tun da fari, wata kungiyar fararen hula mai suna YIAGA Africa, ta yi tsokaci kan yadda aka gudanar da zabe a yankin Ogori/Mangogo.
Mutane da dama sun koka kan magudin zabe a wasu sassan jihar Kogi.
Shi ma dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Mukhtar Ajaka, ya caccaki INEC kan yadda aka gudanar da zaben.
Ajaka ya ce tun kafin a fara kada kuri’a ma’aikatan INEC suka rubuta sakamakon zaben suka bai wa gwamna mai barin gado, Yahaya Bello.