Dino Melaye ya kama hanyar adabo da Majalisa
Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC, wanda shi ne abokin takarar Sanata Dino Melaye, na jam’iyyar PDP, a zaben kujerar Majalisar Dattawa na yankin Kogi ta Yamma ya kama hanyar lashe zaben da aka yi jiya – inda suka fafata a zaben. Sakamakon zaben Kanana Hukumomi 6 cikin 7 na mazabar sun bayyana, kamar yadda hukumar […]
Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC, wanda shi ne abokin takarar Sanata Dino Melaye, na jam’iyyar PDP, a zaben kujerar Majalisar Dattawa na yankin Kogi ta Yamma ya kama hanyar lashe zaben da aka yi jiya – inda suka fafata a zaben.
Sakamakon zaben Kanana Hukumomi 6 cikin 7 na mazabar sun bayyana, kamar yadda hukumar zaben ta kasa, INEC ta sanar.
Ga yadda INEC ta sanar da sakamakon kamar haka:
Sakamakon Karamar Hukumar Ijumu
APC – 11,425
PDP – 7,587
Sakamakon Karamar Hukumar Kabba/Bunu
APC – 15,037
PDP – 8,974
Sakamakon Karamar Hukumar Yagba ta Gabas
APC – 6,633
PDP – 7,745
Sakamakon Karamar Hukumar Mopa/Muro
APC – 4,874
PDP – 3,704
Sakamakon Karamar Hukumar Yagba ta Yamma *
APC – 7,868
PDP – 8,860
Sakamakon Karamar Hukumar Kogi
APC -14,168
PDP – 9,784.