Diphtheria: Cutar mashaƙo ta yi ajalin mutum 10 a Jigawa

Ma’aikatar Lafiya ta ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba a taɓa yin riga-kafin ta ba.

Diphtheria: Cutar mashaƙo ta yi ajalin mutum 10 a Jigawa

Jigawa a taswira

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar nan ta mashaƙo da ake kira Diphtheria a kananan hukumomi 14 na Jihar Jigawa.

Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.

Babban Sakatare a ma’aikatar, Dokta Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.

Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.

A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.

Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kauce wa yaɗuwar cutar.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024