Dirar jami’an ICPC a Jigawa: Shugabannin kananan hukumomi sun tare a ofishin Kwamashina

Shugabannin kananan hukumomin Jihar Jigawa sun kaurace wa kananan hukumominsu yayin da hankalin manyan daraktoci da Kwamashinan kananan Hukumomi na Jihar ya tashi sakamakon binciken da Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (ICPC) ta kaddamar kan yadda kananan hukumomin jihar suka kashe kudadensu. Kwamashinan kananan Hukumomi na Jihar, Alhaji Salisu Sale Indirawa wanda ya […]

Dirar jami’an ICPC a Jigawa: Shugabannin kananan hukumomi sun tare a ofishin Kwamashina
Dirar jami’an ICPC a Jigawa: Shugabannin kananan hukumomi sun tare a ofishin Kwamashina

Shugabannin kananan hukumomin Jihar Jigawa sun kaurace wa kananan hukumominsu yayin da hankalin manyan daraktoci da Kwamashinan kananan Hukumomi na Jihar ya tashi sakamakon binciken da Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (ICPC) ta kaddamar kan yadda kananan hukumomin jihar suka kashe kudadensu.

Kwamashinan kananan Hukumomi na Jihar, Alhaji Salisu Sale Indirawa wanda ya tabbatar da zuwan masu binciken wadanda da kyar suka ba shi damar yin Sallah tunda suka saka shi a gaba da yi masa tambayoyi.
Lokacin da manema labarai suka nemi ya yi musu karin bayani a kan ganawar da suke yi da jami’an na ICPC, ya ce ba zai iya cewa komai ba sai ya kammala ganawa da bakin da suka ziyarce su domin gudanar da bincike.
Wakilinmu ya ziyarci kananan hukumomin Buji da Jahun da Maigatari da Kirikasamma da Dutse ya iske ba kowa a cikin jami’an kananan hukumomin, sun tare a ofishin Kwamashinan suna neman hanyoyin kare kansu.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa an turo jami’an ne na ICPC ne daga Abuja su binciki yadda suka sarrafa kasonsu na tarayya daga shekarar 2007 zuwa bana.
Wani ma’aikaci a ofishin Kwamashinan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce zuwan jami’an na ICPC ya tada wa ma’aikata da jami’an kananan hukumomin jihar 27 hankali. “Kuma hakan yana da nasaba da zaman doya da manja da gwamnatin jihar ke yi da Gwamnatin Tarayya,” inji shi.
Sai dai wani jami’i na hukumar ta ICPC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce zuwansu jihar ba ya da alaka da siyasa, aikinsu ne su yi bincike su tabbatar da gaskiya. Ya ce ana zargin an yi sama-da-fadi da dukiyar gwamnatin jihar a zaben cike-gurbi da aka yi kwanan baya a karamar Hukumar Ringim inda aka umarci kananan hukumomin jihar su hada wasu kudade da aka yi amfani da su wajen karkata akalar zaben, kuma ga zaben kananan hukumomi na zuwa a watan Janairun badi.