Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas
Wata majiyar soji ta ce motar ta kutsa cikin taron sojojin, inda ta kashe wasu daga cikin su nan take.
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin direba ne da ya bugu cikin barasa ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas.
Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu.
- Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa
- Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya
Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin.
Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya, ta sanar a ranar Alhamis cewa za ta fara gudanar da tattakinta a yankin na farko, na kowace shekara a yau Juma’a.
Tattakin mai tsawon kilomita 15, wanda aka dakatar sakamakon wannan mummunan al’amari, ya kamata ya ratsa sassan babban yankin da tsibirin Legas.
Sanarwar ta kuma gargaɗi mazauna yankin da su kwantar da hankulan su domin tattakin da aka saba yi na atisayen soji ne.
Wata majiyar soji ta ce motar ta kutsa cikin taron sojojin, inda ta kashe wasu daga cikin su nan take.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, tun daga lokacin aka kama direban.
Sai dai majiyar ba ta bayyana inda ake tsare da mutumin domin amsa tambayoyi ba.
Wani ganau ya ce, “Tattakin hanyar ya tsaya kwatsam sakamakon lamarin. Ba zan iya bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ba, amma sojoji da dama sun samu munanan raunuka yayin da wasu ’yan ƙalilan suka mutu.”