Direba da ustaz
Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan an cika mota da fasinja sai ustaz ya ce su kawo kudin mota. Da aka fara bashi kudin, sai ya shafa aljihu domin ya ba wani mutum canji sai ya […]
Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan an cika mota da fasinja sai ustaz ya ce su kawo kudin mota. Da aka fara bashi kudin, sai ya shafa aljihu domin ya ba wani mutum canji sai ya ji babu kudin da suka yini suna aiki a aljihun, wani ya sace. Nan da nan sai ya fara kabbara da karfi, ya ce: “Allahu akbar, wani ya cuci kansa!” Direba ya juyo ya ce: “Ustaz, yaya aka yi ne?” Shi kuwa ya ce: “Ai duk cinikin da muka yi yau, wani ya sace su.” Direba ya ce: “Ka ce ya cuci kansa ko dai ya cuce mu?”
Daga Khalil Muhammad, 08031908918