Direba ya amsa laifin kisan uwar dakinsa

Hukumar Tsaron kasa (SSS) da ke yankin Birnin Tarayya Abuja ta gabatar da wasu mutum hudu da ake zargi da sacewa da kuma kashe wata ’yar kasuwa mai suna Misis Edith Chinedu Aliyu, mai makarantun Chelson Group of Schools kuma shugabar bankin ba da rancen gudanar da sana’o’i na Grant Micro Finance Bank da ke […]

Direba ya amsa laifin kisan uwar dakinsa
Direba ya amsa laifin kisan uwar dakinsa

Hukumar Tsaron kasa (SSS) da ke yankin Birnin Tarayya Abuja ta gabatar da wasu mutum hudu da ake zargi da sacewa da kuma kashe wata ’yar kasuwa mai suna Misis Edith Chinedu Aliyu, mai makarantun Chelson Group of Schools kuma shugabar bankin ba da rancen gudanar da sana’o’i na Grant Micro Finance Bank da ke Gwagwalada.
Mataimakin Daraktan Ayyukan na Hukumar Ibrahim Halilu ya ce direban marigayiyar mai suna Ali Angba ne ya bayyana wa hukumar yadda suka sace uwardakin tasa tare da taimakon wasu mutum uku wato; Madwell Ajukwu da Solomon Amodu da kuma Sunday Jacob.
Maitaimakin Daraktan ya bayyana cewa an sace Misis Chinedu ne da misalin karfe 11:55 na daren ranar 29 ga watan Yuni a gidanta da ke Gwagwalada kuma bayan kimanin sa’o’i biyu da sace ta ne aka yi mata kisan gilla, inda daga bisani suka binne ta a dajin ’Yangoji da ke hanyar Abuja zuwa Lakwaja.
Ya kara da cewa: “Washegari sai wadanda suka aikata wannan danyen aiki suka tuntubi danginta suna bukatar Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa kafin sallamarta, duk da cewa sun riga sun kashe ta. A ranar 6 ga watan Yuli ne kuma ’yan uwan marigariyar suka ajiye wa mutanen Naira miliyan biyu da aka canja zuwa Dalar Amurka, ya kama Dala 11,550 a kusa da Titin Obajana da ke garin Lakwaja ba tare da sun sanar wa hukuma ba.”
A lokacin da suke amsa tambayoyin manema labarai, wadanda ake zargin sun amsa laifuffukansu. Kodayake sun ce wanda ya kashe matar shi ne wani mai suna Douglas wanda aka fi sani da Doggy.
daya daga cikin mutanen da ake zargin, Madwell Ajukwu mai shekara 41 wanda ya kare karatun digirinsa daga Jami’ar Nsukka da ke Jihar Enugu, ya amsa laifinsa a lamarin sace matar. Ya ce: “Mu ne muka sace ta, amma da fari ba mu da niyyar kashe ta saboda direbanta ya ce ne kawai mu yi garkuwa da ita. Amma a kan hanyarmu ta kai ta maboya ne ta yanke jiki ta fadi. Daga nan kuma direbanta ya umarce da mu kashe ta saboda yadda ta shaida fuskokinmu wasunmu, gudun kada ta gane mu daga baya.”
Ya ce: “Wani Douglas ne ya kashe ta amma ba ya nan tare da mu. Ni da Solomon ne muka haka kabarin da aka binne ta.”
Madwell ya ce marigayiyar ta gane shi ne saboda kwanaki biyu kafin faruwar lamarin, direbanta ya kai shi gidan domin yin leken asiri a wani mataki na shirye-shiryen sace ta. Ya ce kafin ya sa hannu a wannan danyen aiki, shi malami ne a wata makaranta da ke Gwagwalada.
Mutum na hudu da hukumar ta gabatar ga manema labarai mai suna Sunday Jacob, ya amsa laifin daukar nauyi da kuma kitsa yadda za su sace matar. Amma ya ce bai da masaniya a kisan marigayiyar wadda a cewarsa ya samu labarin rasuwarta ne lokacin da yake hannun jami’an tsaro. Ya kara da cewa direbanta Ali ne ya bayyana masa cewa uwardakinsa tana da kudi kuma ya ba da shawarar mu sace ta.
Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida, Solomon Amodu wanda dalibi ne da ke shekarar karshe a Jami’ar Abuja ya ce akwai hannusa a kisan matar. Solomon wanda shi ya tuka motar da aka sanya matar a ciki bayan sun sace ta, ya ce: “A daidai lokacin da muka isa wani shingen bincike ne muka tube takunkumin da muka sanya a fuskokinmu. A nan ne ta shaida fuskar Madwell, inda ta ce shi ne mutumin da Ali ya zo da shi gidanta kwanakin baya, tana fahimtar haka sai ta kidime ta suma.”
Madwell ya kira Ali ta waya ya shaida masa abin da ke faruwa. A cewarsa “Sai Ali ya ba da umarnin kashe ta.”
“Doggy ya umarce ni da na daure mata hannuwa, shi kuma ya shake ta har ta mutu,” inji shi.
Direban marigayiyar Ali,  mai kimanin shekara 27 ya amsa laifin shirya sace uwardakin nasa. Amma ya musanta cewa shi ne ya ba da umarnin a kashe ta. Kuma ya ce ya karbi Naira dubu 199 ne kawai daga cikin kudin fansar da suka karba daga iyalan marigayiyar.
Hakazalika, Madwell ya ce ya karbi Naira dubu 500 ne akwai da kuma wata Naira dubu 500 da ya ba Douglas, mutumin da bai kai ga shiga hannu ba tukuna. Shi kuwa Solomon ya ce ba a ba shi ko sisin kwabo ba daga kudin ba.
Wani dan uwan matar da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce sun biya Naira miliyan biyar a kokarin fanso ’yar uwarsu. Ya ce sun shigo da jami’an tsaro ne cikin lamarin bayan da suka fahimci cewa wadanda suka yi garkuwa da ita sun ki su sada su da ’yar uwar tasu ta waya, abin da zai tabbatar da cewa tana raye.