Direba ya kashe ɗan sanda a Ekiti

Wani direban mota ya kashe wani ɗan sanda mai muƙamin mataimakin sufeton ‘yan sanda (ASP) da ke aiki da rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti. Bayanai sun ce direban wanda tsere ya murƙushe jami’in ɗan sandan mai suna Idris Lawal har lahira a wani shingen binciken ababen hawa da ke garejin Ayemi daura da titin Iworoko […]

Direba ya kashe ɗan sanda a Ekiti

Wasu ’yan sandan Najeriya a bakin aiki

Wani direban mota ya kashe wani ɗan sanda mai muƙamin mataimakin sufeton ‘yan sanda (ASP) da ke aiki da rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti.

Bayanai sun ce direban wanda tsere ya murƙushe jami’in ɗan sandan mai suna Idris Lawal har lahira a wani shingen binciken ababen hawa da ke garejin Ayemi daura da titin Iworoko a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da aikin bincike da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin.

Duk da cewa an garzaya da jami’in zuwa Asibitin Koyarwa na Jihar Ekiti (EKSUTH) don duba lafiyarsa, likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da rasuwarsa.

Sanarwar da ’yan sanda suka fitar ta bayyana cewa direban yana cikin wata farar motar ƙirar  Marsandi da ke tsala gudun wuce sa’a.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike a ƙoƙarinta na cafke mai laifin.