Direba ya kashe matarsa da `ya `yansa 2 a Edo

Hukumar `yan sandan jihar Edo ta tsare wani direba mai suna Uwaila Idehen dan shekara 35 akan tuhumarsa da laifin kashe matarsa da kuma `ya `yansu biyu. Kwamishinan `yan sandan jihar Edo Hakeem Olusegun Odumosu ya ce,  Uwaila na daya daga cikin mutum 110 da ake zarginsu da aikata laifuka a jihar  da aka gurfanar […]

Direba ya kashe matarsa da `ya `yansa 2 a Edo

Hukumar `yan sandan jihar Edo ta tsare wani direba mai suna Uwaila Idehen dan shekara 35 akan tuhumarsa da laifin kashe matarsa da kuma `ya `yansu biyu.

Kwamishinan `yan sandan jihar Edo Hakeem Olusegun Odumosu ya ce,  Uwaila na daya daga cikin mutum 110 da ake zarginsu da aikata laifuka a jihar  da aka gurfanar da su.

Kwamishinan ya ce, wadanda ake zargin an tsare su ne akan wasu laifuka da suka hada da: tsafi da fashi da makami, yin garkuwa da mutane, sace-sace da kuma aikata fyade.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta