Direba ya mutu a hadarin tankar mai a Abaji
Wani direban tankar mai rasu sanadiyyar hadarin motar tankar mai tare da raunata wasu mutum uku lokacin da tankar man ta yi hadarin a kusa da gadar Abaji da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja. Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da tsakar dare ranar Asabar lokacin da direban tankar mai lamba JJJ 198 […]
Wani direban tankar mai rasu sanadiyyar hadarin motar tankar mai tare da raunata wasu mutum uku lokacin da tankar man ta yi hadarin a kusa da gadar Abaji da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da tsakar dare ranar Asabar lokacin da direban tankar mai lamba JJJ 198 XB ta kauce hanya.
Jami’an kashe gobara sun ce, sun kawo dauki ne lokacin da suka samu rahoton hadarin daga hukumar kiyaye hadurra ta kasa. Rahotan na cewa, tankar ta yi hadarin ne sanadiyyar barcin da ya kwashe shi direban.