Direba ya take soja har lahira a Legas
Direban ya tsere da matarsa, amma wasu sojoji da abin ya faru a kan idonsu suka bi shi suka kamo shi
Direban babbar motar wani kamfanin jigila ya take wani soja har lahira a kan babban titin Badagry da ke Jihar Legas.
Motar ta bi ta kan sojan ne a lokacin da direbanta yake kokarin tserewa daga masu tatsar kudi daga masu motocin haya a Orile Bus Stop da ke yankin Iganmu.
Wani mai sana’ar tireda a Orile, Shola James, ya ce “tayar motar ta baya ce ta muttsike kan sojan, abin ba kyan gani.”
Shola ya ce direban ya tsere amma wasu sojoji da abin ya faru a kan idonsu suka bi shi suka kamo shi a tashar motar Mile 2.
Ya ce sojojin sun tusa keyar direban da motar zuwa inda abin ya faru amma yaron motar ya tsere.
Wani mai sana’ar faci a Orile ya ce sojan ya gamu da karar kwana ne a lokacin da yake kan baburinsa.
Amma kakakin ’yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da abin da ya faru, amma ya ce ba a damka musu motar ko direban da ake zargi ba.
A cewarsa, “bayan faruwar lamarin, DPO na Orile da jami’ansa sun je wurin inda suka ga gawar sojan.
“Sojoji sun dawo da direban da motar, amma bariki suka wuce da su tare da gawar sojan.”