Direban bas ya mayar da N10m da gwala-gwalai da ya tsinta

Direban ya tsinci tsabar kudi $20,000 da N500,000 da gwala-gwalai a motarsa.

Direban bas ya mayar da N10m da gwala-gwalai da ya tsinta

Wani direban bas ya mayar wa fasinjansa tsabar kudi da gwala-gwalai da kimarsu ta haura Naira miliyan 10 da ya manta da su a motar direban.

Jakar da fasinjan ya manta a cikin bas din na dauke da tsabar kudi Dala 20,000 da Naira 500,000, da gwala-gwalai da wayar hannu kirar Samsung Note 20 Extra, da cekin kudi.

Akwai kuma sauran abubuwa masu daraja da suka hada da agoguna guda tara da wata sarka.

Mai jakar ya manta da ita ne a cikin bas din da ke daukar fasinja zuwa cikin filin jirgi sama a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

Hukumar kamfanin BASL da ke kula da bangaren da lamarin ya faru a filin jirgin ta ce ta gano cewa jakar mallakin wani babban mutum ne da ke hanyarsa ta zuwa Fatakwal daga Legas, a ranar Litinin.

Jami’in Hulda da Jama’a na BASL, Mikail Mumuni ya ce fasinjan ya manta da jakar ne a cikin bas kirar Coaster da ta dauki fasinja kafin su hau jirgi.

Daga baya direban bas din, Emmanuel Eluu, ya tsinci jakar, ya kaita wa babban jami’in kula da tsaro, Taiwo Adelakun.

Sai “aka hada shi da Babban Majanan Kula da Ayyuka, Gbadamosi Olasunkami da kuma Oluwole Alonge suka abincika suka tabbatar da abubuwan da ke cikin jakar sannan aka adana,” inji Mumuni.

Mumini ya ce abubuwan da ke cikin jakar sun hada da wasu gwala-gwalai a cikin kananan jakunkuna da bandir biyu na Dala 20,000 da bandir biyar na N5,0000 da wayar Samsun Note 20 Extra da aguguna tara a cikin kanan jakuna bakake da ruwan kwai, kayan yari da cikin kananan jakuna masu ruwan gwal, cekin banki guda hudu da sauransu da ambulan iri-iri da tabarau da kuma maganin ido sai katin shaidar mai jakar.

Mumini ya ce, “Adelakun ya adana kayan isa umarnin Manajan Tsaron filin jirgin, Okeowo Olatunbosun da kuma Gbadamosi Olasunkanmi a matsayin shaida.”

Shugaban tsaron filin jirgin ya yi amfani da lambar mai jakar da aka gani a jikin katinsa ya kira shi ta waya.

Da mai jakar ya sauka a Fatakwal sai ya tura wani hadiminsa ya je ya karbi jakar a madadinsa.

“Mai jakar ya kira Adelakun (shugaban tsaro) ta bidiyo inda ya tabbatar musu cewa shi ne ya tura hadimin nasa, ya kuma yi godiya ga hukumar Filin Jirgin Murtala Mohammed bisa rikon amana da kwarewa da suka nuna,” inji Mumuni.

A watan Afrilun bana, irin haka ta taba faruwa a filin jirin na Legas, inda aka tsinci Naira miliyan 2.3 da ka hanyarsa ta zuwa Uyoa a jirgin Ibom Airline, aka kuma mayar masa da kudin nasa.

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa

Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero