Direban Keke Napep ya mutu yana kwance a cikin kekensa

Wani direban babur mai kafa uku (Kake Napep) a Abuja, mai suna Mamuda Muhammad, ya rasa ransa a lokacin da ya ke kwance a cikin kekensa  inda aka jini yana fitowa ta bakinsa da kuma hanci. Marigayin wanda dan asalin Karamar Hukumar Sabuwa ne a jihar Katsina ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta […]

Direban Keke Napep ya mutu yana kwance a cikin kekensa

Tarin baburan Keke Napep a tasharsu ta Gwarimpa bayan fara aikin dokar hana tukin.

Wani direban babur mai kafa uku (Kake Napep) a Abuja, mai suna Mamuda Muhammad, ya rasa ransa a lokacin da ya ke kwance a cikin kekensa  inda aka jini yana fitowa ta bakinsa da kuma hanci.

Marigayin wanda dan asalin Karamar Hukumar Sabuwa ne a jihar Katsina ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta gabata a cikin keken a inda ya saba ajiyeta a wani garejin kekuna da ke mahadar Kabusa da ke yankin Apo Abuja.

Shugaban Kungiyar masu sana’ar na yankin malam Yusuf Muhammad, ya shaidawa Aminiya cewa, marigayin wanda ke fama da matsalar cutar hawan jini gabanin rasuwarsa, da farko ya ajiye aiki ne tun a ranar Alhamis da ta gabata a sakamakon kama baburansu da ya ce ‘yan sanda ke yi a yankin biyo bayan dokar hana tukin baburan a Abuja.

Ya ce, ‘yan sandan na kamen ne duk da basu damar aiki da jami’an VIO su ka yi masu a yankin na Kabusa da kuma Galadimawa da ke inda su ke karban Naira dubu 3 zuwa dubu 5 a cewarsa kafin su bada belin kekunan.

Ya ce, bayan an sanar da shi labarin mutuwar ya garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda inda su ka je su ka dauki hoton gawar tare da rubuta bayanin akanta da ya basu damar daukanta zuwa yankinsa na asali inda aka  binne gawar.

Da aka tuntube shi babban jami’in ‘yan sanda na Apo CSP Emega John, ya tabbatar da faruwar lamarin.