Direban mota ya kashe kansa a daki a Bayelsa

Wani direban babbar mota, mai shekaru 45, ya rataye kansa cikin daki, inda nan ta ke ya mutu. Lamarin ya faru ne a kauyen Etegwe na Karamar hukumar Yenagoa, cikin Jihar Bayelsa. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya bayyana sunan mutumin Oliver Osieme, dan asalin jihar Anambra, ya aikata hakan a daren jiya Litinin. […]

Direban mota ya kashe kansa a daki a Bayelsa

Rataya

Wani direban babbar mota, mai shekaru 45, ya rataye kansa cikin daki, inda nan ta ke ya mutu.

Lamarin ya faru ne a kauyen Etegwe na Karamar hukumar Yenagoa, cikin Jihar Bayelsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya bayyana sunan mutumin Oliver Osieme, dan asalin jihar Anambra, ya aikata hakan a daren jiya Litinin.

Bayanai sun ce, ya rataye kan nasa ne yayin da mai dakinsa, wadda take da kasuwanci da kuma sauran ‘yan uwansa na kusa suka fita wajen harkokinsu na kasuwanci.

Lamarin ya jefa makwabta da sauran mazauna wurin cikin yanayin makoki.