Direban tanka ya shiga hannu bayan hallaka mai babur har lahira a Legas
Hukumar ta ce ta miƙa direban hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
An kama wani direban tanka bayan ya yi ƙoƙarin tserewa biyo bayan buge wani ɗan aiken saƙo a babur, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa a titin Kpdesho da ke Jihar Legas.
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA), ta ce hatsarin ya faru ne lokacin da tankar man mai lamba T-19089LA, wadda ke ɗauke da lita 33,000 na man gyaɗa, ta buge mai babur ɗin, wanda ya rasu nan take.
- ’Yan sanda sun kama mutum 5 bayan daƙile harin ’yan bindiga a Sakkwato
- Matatar Dangote ta dawo sayar da fetur da Naira
Babban Manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce direban ya yi ƙoƙarin guduwa daga wajen ba tare da ya taimaka wa mamacin ko ya kai rahoton abin da ya faru ga jami’an da abin ya shafa ba.
Ya ce bayan samun rahoton hatsarin, jami’an LASTMA suka bi sahun direban, suka kama shi tare da ƙwace tankar.
Bakare-Oki, ya ƙara da cewa an miƙa direban da motar ga Sashen Kula da Cunkoson Ababen Hawa na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas (STD) da ke Ikeja, domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.