Direbobin dakon kaya zuwa Kudu sun koka da jami’an tsaro
Direbobin daukar kaya da ke safara daga Jihar Filato zuwa sassan Kudu na kungiyar direbobi ta Nijeriya (NURTW) sun koka da yadda jami’an tsaro ke janyo wa wasu daga cikin ’ya’yan kungiyarsu suke rasa ayyukansu daga wajen iyayen gidansu, sakamakon tatsar da suke musu a manyan hanyoyin kasar nan.Direbobin sun bayyana kukan nasu ne a […]

Direbobin daukar kaya da ke safara daga Jihar Filato zuwa sassan Kudu na kungiyar direbobi ta Nijeriya (NURTW) sun koka da yadda jami’an tsaro ke janyo wa wasu daga cikin ’ya’yan kungiyarsu suke rasa ayyukansu daga wajen iyayen gidansu, sakamakon tatsar da suke musu a manyan hanyoyin kasar nan.
Direbobin sun bayyana kukan nasu ne a wata ganawa da Aminiya a Kalaba a makon da ya shige, inda wani direba mai suna Ahmad Sa’id Muhammad ya ce ya shafe shekara goma yana sana’ar tuki kan manyan hanyoyin kasar nan, amma ya nuna mamakinsa kan yadda daga Jos zuwa Kalaba, “Naira dubu goma ta kare wajen raba wa jami’an tsaro na goro? Gaskiya a kawai matsala sosai,
domin sun mayar da shi kamar doka, idan direba ya zo, dole sai ya bayar da kudi ko kuma a ajiye shi gefen hanya na tsawon wasu awoyi, a ci ma mutum mutunci, a bata masa lokaci. Kuma shingayen suna da yawa kwarai. Abin ya zama kamar ka’ida domin akwai masu karbar Naira 300; akwai Naira 200; akwai kuma Naira 100, kuma ba su yi mana bayanin dalilin da ya sa suke karbar wannan kudi.” Inji shi.
Shi kuwa Surajo Ibrahim, wani direba da yake bin hanya daga Jos zuwa Legas da kuma Fatakwal kai kayan tumatir da sauran kayan rafi, ya bayyana irin wahalar da suke sha a hannun jami’an
tsaron ‘wajen yin saitin hanya’.
Ya ce wani abin takaicin shi ne duk da shingayen da ake sanyawa hanya, ba su hana yin fashi da makami ba, inda har mutane ke rasa rayukansu banda dukiya.
Shi ma direba Mohammed Auwal ya yi nasa bayanin, wanda bai saba da na sauran direbobi ba, game da matsalar da ke shiga tsakaninsu da masu gidansu da suke wa tukau.
Yayin da wakilinmu ya bukaci jin ta bakin jami’an tsaro ya je hedkwatar rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba, inda ya sadu da mai magana da yawunta, DSP Hogan Bassey ya shaida masa cewa ba su da masaniyar haka, domin babu wanda ya taba kai musu kukan haka, amma za su yi bincike.
Sannan shi kuma Mista Jonathan Johnson, Mataimakin Babban Baturen ’Yan Sanda (AIG), mai kula da shiyya ta shida da ke Kalaba ya ce bai taba samun labarin abin nan yana faruwa ba, “Domin kamar yadda na taba gaya maka kwanan baya da na dawo daga ziyarar ofisoshi da rundunoni da ke karkashina, duk wani wanda aka samu ko aka kama da laifin karbar hanci da rashawa, za a gurfanar da shi gaban kotu kuma za a tube masa kaya. Don haka rundunata ba ta da masaniya kuma ba ta aiki kowa ya yi haka ba”. Inji shi.