Abin da ya sa direbobin J5 zanga-zanga a Binuwai
Deribobin sun bukaci gwamnatin jihar Benuwai ta shiga lamarin.
Direbobin motocin J5 da ke daukar kayan gwari daga garin Gboko na Jihar Binuwai zuwa sassa daban-daban na kasar nan sun yi zanga-zanga tare da tare babbar hanyar shiga garin.
Direbobin sun ce sun yi zanga-zangar ne sakamakon tursasawar da matasan yankin ke yi musu suna karbar kudi a hannunsu.
Da yake zantawa da Aminiya kan lamarin, Shugaban Kungiyar Direbobin Motocin J5 na garin Gboko, Malam Muhammed Mahe Alhassan Kwaftara, ya yi karin haske a kan dalilin zanga-zangar.
- Matsalar Tsaro: An bukaci Fulani makiyaya su yi wa dabbobinsu lamba
- An kama ‘barawo’ yana bikin zagayowar ranar haihuwarsa
“Akwai wata kasuwa a hanyar Ribas zuwa Binuwai; idan direba ya dauko kaya sai ya hadu da shingayen wadannan matasa ‘yan iska sama da 20 kuma duk shinge sai ya biya kudi N5,000 kafin ya wuce ko kuma a yi masa duka.
“Mun kai kokenmu ga jami’an tsaro da sarakunan wannan yanki don a dauki mataki kan wannan al’amari amma ba a iya yin komai ba.
“Don haka muka fito wannan zanga-zanga har sai Gwamna ya zo ya ga abin da yake faruwa, don ya dauki mataki.
“Don mu ma ‘yan Najeriya ne, muna da hakki a kansa na ya kare mu,” a cewar Mahe.
‘Sai Gwamna ya zo’
Ya ce sun shiga zanga-zangar ne saboda kayar da motarsu da matasa masu saka shinge suka yi a kan hanyar Ribas zuwa garin na Gboko.
Ya kuma ce faduwar motar ta haddasa wa mutanen da ke ciki munanan raunuka lokacin da lamarin ya faru.
Mahe ya bayyana cewa a kullum sukan yi safarar kayan gwari mota 150 zuwa 200, zuwa garuruwan Kano, Maiduguri, Katsina, Sakkwato, Fatakwal, Kalaba da sauran sassa na Najeriya.
Ya ce amma babbar damuwarsu a garin ita ce matasa na cin zarafin direbobinsu, ta hanyar sanya masu shingaye a kowanne kauye inda suke karbar kudade daga wajensu.
Direbobin motocin na J5 sun fito da motocinsu ne suka rufe babbar hanyar shiga garin, da misalin karfe 6 na safiyar ranar Laraba har zuwa wayewar ranar Alhamis.
Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, Sewuese Kate Anene, ta waya don jin ta-bakinta kan al’amarin.
Amma ta aiko da rubutaccen sako ta waya cewa zuwa wannan lokaci ba ta samu labarin faruwar lamarin ba.