Direbobin J5 sun koka da yawan fashi a hanyar kwoi zuwa Jere

kungiyar Direbobin Motocin J5 ta koka kan yawan fashin da ake yi wa ’ya’yanta a hanyar da tashi daga Kwoi da Jere a Jihar Kaduna a hanyarsu ta zuwa Legas.  Shugaban kungiyar na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Malam Mahe Kwaftara ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.Ya ce “Direbobinmu […]

Direbobin J5 sun koka da yawan fashi a hanyar kwoi zuwa Jere
Direbobin J5 sun koka da yawan fashi a hanyar kwoi zuwa Jere

kungiyar Direbobin Motocin J5 ta koka kan yawan fashin da ake yi wa ’ya’yanta a hanyar da tashi daga Kwoi da Jere a Jihar Kaduna a hanyarsu ta zuwa Legas. 

Shugaban kungiyar na karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Malam Mahe Kwaftara ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce “Direbobinmu na J5 masu tafiyar dare daga Arewa zuwa Legas da sassan kudancin kasar nan, suna samun matsala a kan hanyar Kwoi zuwa Jere. A kullum barayi suna tare direbobinmu a dajin yankin suna kayar mana da motocinmu tare da harbe direbobinmu.”
Ya ce ko a makon jiya barayin sun kashe direbansu mai suna Abdullahi Manguna, kuma sun kayar musu da motoci biyar, inda a bana suka kayar musu da motoci sama da 20.
“Wadannan barayi sukan tare hanyar su bude wa motocinmu wuta duk da akwai wuraren binciken motoci na sojoji guda biyu da na yan sanda biyu a hanyar Kwoi zuwa Jere. Amma barayin suna tsayawa a tsakanin wuraren bincike su kayar mana da motoci su yi mana fashi,” inji shi.
Ya roki gwamnatin Jihar Kaduna ta taimaka musu ta sanya ido a wuraren ta hanyar kara tura jami’antsaro a yankin don kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.