Direbobin kanta sun toshe hanyar Minna-Bida

Direbobin manyan motoci sun tare babbar hanyar Minna zuwa Bida da ke Jihar Neja kan zargin ‘yan sanda da cin zalinsu

Direbobin kanta sun toshe hanyar Minna-Bida

Direbobin manyan motoci sun tare babbar hanyar Minna zuwa Bida da ke Jihar Neja kan zargin ‘yan sanda da cin zalinsu a kan hanyar.

Aminiya ta gano cewa bin da ‘yan sanda masu sintiri a kan hanyar suka yi wa wani direban kanta da ke kokarin tsere musu daga Paiko ya sanya motarsa ta yi ha a daidai shataletalen Kpakungu a garin Minna.

Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa wata motar ‘yan sanda ta lalace a sakamakon hatsarin, kuma a lokacin da wakilinmu ya isa wurin, direban kantar yana tsare a ofishin ‘yan sanda na tashar motar Kpakungu.

Bayan haka ne sauran direbobin kanta da suka iso wurin suka tare hanyar da cewa dole sai an sako abokin aikinsu.

Yaron motar da ta yi hatsari, Abubakar Adamu ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan sanda sun nemi mai gidan nasa ya ba su na goro a Paiko, kilomita 15 kafin shiga Minna, inda “muka ba su N500 amma suka ki karba; muka cika musu ya kai N1000 amma duk da haka suka ki.

“Shi ne muka wuce, amma suka biyo mu, har har sai da muka zo Minna, inda suka yi aron hannu za su tare mu, wanda hakan ya sa motarmu ta yi hatsari.

“Motarmu ta kusa take wani mahaukaci da ke kwance a gefen titi, amma Allah Ya kiyaye.”

Da aka tambaye shi ko suna sane cewa ‘yan sandan sun biyo su, sai ya ce, “Mun sani, amma ba mu da isassun kudin da za mu ba su.

“Haka suke yi suna tatsar kudade a hannunmu a kwana biyu da muka yi a kan hanyar, inda muka kashe makudan kudade kan gyaran motar, saboda lalacewar da ta rika yi.”

Abubakar ya bayyana cewa sun dauko barkono ne daga Azare a Jihar Bauchi za su kai Legas, hakan ta faru.

Wakilinmu ya yi kokarin yin magana da kakakin ‘yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, amma hakan bai samu ba; ya kira wayarsa kuma, amma tana kashe.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya