Direbobin Kudu sun koka kan zaman kullen IPOB

Suna rokon gwamnati ta ba su tallafi saboda asarar da IPOB ke ja musu.

Direbobin Kudu sun koka kan zaman kullen IPOB

‘Yan awaren Biyafara na IPOB

Direbobi a yankin Kudu sun bukaci a rika ba su tallafi saboda zaman gida da haramtacciyar kungiyar IPOB ke tilasta musu a duk ranar Litinin.

Direbobin sun bukaci gwamnati ta rika ba su tallafin ko kuma su ’yan IPOB din saboda mawuyacin halin da suke tsintar kansu a ciki a lokacin zaman gidan.

Direbobin sun yi wannan kiran ne a yayin da suke zantawa da manema labarai a Umuahia babban birnin Jihar Abia a kan irin illar da zaman gidan ke haifar wa ga kasuwancinsu.

“Muna bukatar a tallafa mana duba da yadda wannan dokar ke hana mutane zirga-ziraga a duk lokacin da aka sanya dokar,” a cewar wasu direbobi.

Suka kara da cewa yawan tilasta musu zaman gida “ba karamar illa take mana a kasuwancinmu ba saboda duk lokacin zaman gidan ba a samun fasinja, ga shi yawancinmu ba motocin kanmu ba ne, karba muka yi mu rika biya a hankali.”

Da dama dai daga cikin direbobin sun ce sun mayar da ranakun zaman gidan a matsayin ranakun hutun dole.