Direbobin manyan motoci sun koka da aiyukan jami’an LASTMA a Legas

Wasdanu direbobin manyan motoci da ke daukar kaya a tashar jiragen ruwa ta Tincan (Tinkan) da ke Apapa sun koka kan yadda jami’an Hukumar Hana Cinkoson Ababen hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ke gudanar da ayyukansu a yankin inda suka zarge su da uzzura musu tare da kama motocinsu da cin tararsu makudan kudi ba […]

Direbobin manyan motoci sun koka da aiyukan jami’an LASTMA a Legas

Wasdanu direbobin manyan motoci da ke daukar kaya a tashar jiragen ruwa ta Tincan (Tinkan) da ke Apapa sun koka kan yadda jami’an Hukumar Hana Cinkoson Ababen hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ke gudanar da ayyukansu a yankin inda suka zarge su da uzzura musu tare da kama motocinsu da cin tararsu makudan kudi ba tare da sun aikata laifi ba.

Daya daga cikin direbobin mai suna Aliyu Muhammad, ya shaida wa Aminiya cewa, kalubalen da direbobin manyan motoci ke fuskanta da zarar sun shiga Legas shi ne kusan duk inda za su taka sai sun biya kudi, “Duk inda za ka shiga dan sanda zai daga maka hannu daga Naira dubu biyu zuwa dubu hudu sai ka ba su, musamman a yankin Apapa. Ba ka kashe kudi ba ka kashe Naira dubu 25 daga Bega zuwa Apapa kafin ka shiga tashar jirgin ruwa ka dauko kaya, sannan jami’an LASTMA duk lokacin da motarka ta tsaya wato ta lalace to ka shiga cikin matsala, domin sai a ci tararka Naira dubu 150, yanzu haka ma a ganina an maida abin kasuwanci ne, ba sa rage cinkoso sai dai hada wa gwamnatin jihar kudi,” inji shi.

Haka shi ma Ibrahim Abubakar da ke tukin babbar mota a garin Legas ya ce, ya kwashe shekara sama da 20 yana aikin mota, inda ya ce, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Legas su rika tsawata wa jami’an LASTMA domin an bar su suna cin karensu ba babbaka,  “Sun sha kama ni suna cin tara, kuma sau tari kudin ba aljihun gwamnati yake shiga ba, kuma ina ganin akwai alamun kabilanci game da yadda suke gudanar da ayyukansu, domin idan motar Bahaushe suka kama ko ta Ibo sun fi tsawwalawa idan suka ga motar dan uwansu Bayarebe ne ba sa takura musu. Don haka fatarmu ya zamana ayyukan kula da ababen hawa da cinkoson su rataya a wuyan jami’an Hukumar Kiyaye Haddura wato ‘Road Safety” inji shi.

Danladi Babalado, kuwa ya shaida wa Aminiya cewa ya kwashe shekara 28 yana  tukin babbar mota, kuma a baya ba su fuskanci matsalar da a yanzu suke fama da ita ba. Ya ce matsalolin sun yi kamari ne shekara biyar zuwa bakwai da suka gabata, “A da za ka shigo Legas cikin kwana daya a yi maka lodi ka tafi amma a yanzu masu dukiya na wahala kuma direbobin a wahala muke. Domin sai mutum ya shigo garin nan ya kwashe mako biyu zuwa wata bai yi lodi ba, sakamakon cin hanci da ma’aikata ke karba. Sun kawo tsarin shiga lilfon kafin ka je ka dauki kaya a tashar ruwa, a lilfon din sai ka yi mako guda ba a kira ka ba. Amma cikin dare sai ka ga an shiga da mota sama da 80 a boye, sannan ga lalacewar hanyoyi, mu yanzu ba mu sani ba, gwamnati tana sane ko kuma ma’aikatanta ne ke yi ba tare da saninta ba?

Suna karbar makudan kudi a wajenmu, ga duka ga cin zarafi ba kuma farfasa mana gilasan motoci da suke yi babu gaira ba dalili, ma’aikaci ya doke ka, ya fasa maka mota sannan ka dauki kudi ka ba shi kana ba shi hakuri. Don haka ya kamata gwamnati ta dubi halin da talakawa ke ciki, yanzu haka nafi kwana 22 da barin gida ina da yaran mota su biyu da kowanne kullum sai na ba su Naira 700 kudin abinci ban da wanda ni zan ci. Ga iyali mun bari a gida yau a aiko ba abinci gobe wane bai da lafiya a haka muke. Babbar matsalarmu jami’an LASTMA yanzu da karfi suke karbe mota su aza maka tara, kuma idan aka kama motarka in an ga kai bako ne sai ka biya daga Naira dubu 109 zuwa dubu 150. Amma idan kai nasu ne Naira dubu 5 zuwa dubu 10 ta raba ka da su, don haka muna fata Gwamnatin Tarayya za ta sanya ido,” inji shi.