Direbobin mayan motoci sun koka biyan kudin harji a jahar Ogun

Direbobin manyan motoci sun koka da yadda suka ce ana addabarsu da karbar kudade na ba-gaira ba-dalili da sunan kudin shaga na  raya kasa. Direbobin sun ce a duk Jahohin da suke Nijeriya babu inda suke cin karo da irin wannan matsaloli fiye da jahar Ogun.Malam Bala Musa, wani tsohon direba ne wanda ya shaida […]

Direbobin mayan motoci sun koka biyan kudin harji a jahar Ogun
Direbobin mayan motoci sun koka biyan kudin harji a jahar Ogun

Direbobin manyan motoci sun koka da yadda suka ce ana addabarsu da karbar kudade na ba-gaira ba-dalili da sunan kudin shaga na  raya kasa.
Direbobin sun ce a duk Jahohin da suke Nijeriya babu inda suke cin karo da irin wannan matsaloli fiye da jahar Ogun.
Malam Bala Musa, wani tsohon direba ne wanda ya shaida wa Aminiya cewa babbar matsalar da suke fuskanta ita ce irin takura da tsangwamar da wasu matasa wadanda ya kira ‘yan zauna gari banza ke addabar su a jahar domin matasan na tursasa su biya naira 1500 ko 2000 koma fiye da haka a wurare daban daban.
Musa ya ce, “a tsakanin unguwar Biju da Lusada sai direba ya kashe naira dubu 5000. Inko baka bayar ba matasan dauke da sanduna su rufe ka da duka kai da yaran motar ka.” Ya ce ya kamata gwamnatin jihar Ogun ta dauki mataki.
Shiko wani matashin direba mai suna Bashir Alasan ya shaidawa Aminiya cewa “a duk fadin Nijeriya ba inda suke fuskantar irin wannan matsalar kamar a jahar Ogun Jahohi irin su Legas da Patakol dama Oyo na da  tsari irin  nasu da basa tada hankula domin a tsare suke nasu ayyukan amma a jahar Ogun a bin nasu yayi tsanani”
Hakan ya sa muka tuntubi shugaban kungiyar direbobin manyan motoci reshen Abbatuwa a Agege, Alhaji Muhammad Bello wanda ya tabbatar mana da irin korafe-korafen da direbobin ke yi. Ya ce sun yi iyakacin kokarinsu don magance matsalar amma hakan ya ci tura.
 “Yawan kudaden rabanu na ci mana tuwo a kwarya, ya za a ce a tafiyar da bata wuce kilomita 20 ba direba ya biya kudin haraji naira dubu 9,000? Ai ka ga abin ya yi yawa tunda dai ba haramtatun kaya muke jigila ba, kaya ne da ake yi a nan jahar Ogun. Bayan ka dauko kafin ka fito a tsakanin karamar hukumomi biyu ka kashe naira dubu 9,000 wannan abu ya kazanta. Kira na ga gwamnati shi ne ta duba wannan lamarin in tana sane to a sassautamana inko ba hannunta a ciki wasu tsirarune ke zaluntarmu suna ci da gumin mu to tayi mana maganinsu domin wannan matsalar  ta dade tana damun mu.” In ji shugaban kungiyar.
Muhammad Auwal wanda dankungiyar direbobin manyar motar ne ya shaidawa Aminiya cewa a yanzu dayawa daga cikin direbobinsu basa ra’ayin  zuwa Jahar Ogun saboda matsalar.