Direbobin tanka sun toshe hanyar Kano-Zariya

Kwana guda bayan zargin soja da harbe wani direban tanka a hanyar Zariya zuwa Kano, direbobin tanka sun rufe hanyar don gudanar da zanga-zanga. Da misalin karfe 3:30 na ranar Laraba ne dai wani soja da ke aiki a wani kamfanin gini ya harbe direban har lahira bayan sun samu sabani a Tashar Yari da […]

Direbobin tanka sun toshe hanyar Kano-Zariya

Kwana guda bayan zargin soja da harbe wani direban tanka a hanyar Zariya zuwa Kano, direbobin tanka sun rufe hanyar don gudanar da zanga-zanga.

Da misalin karfe 3:30 na ranar Laraba ne dai wani soja da ke aiki a wani kamfanin gini ya harbe direban har lahira bayan sun samu sabani a Tashar Yari da ke Makarfi, kusa da babbar hanyar.

Duk kokarin da ’yan sanda da Kungiyar Ma’aikatan Sufuri (NURTW) na bude hanyar tun a ranar Laraba ya ci tura, direbobin tankar sun ki janye motocinsu.

Kwamandan Hukumar kiyaye Haddura na shiyyar, Lawal Garba, ya ce duk da ba su gano musabbabin zanga-zangar ba, bincikensu ya tabbatar da an harbe direban tankar.

“Wannan lamari dai  bai yi dadi ba, domin tun ranar Laraba abu ya ki ci, ya ki cinyewa; mutane na shan wahala sakamakon hakan”, a cewarsa.

Sai dai ya ce hukumar na ci gaba da kokarin shawo kan lamarin, da taimakon sauran masu ruwa da tsaki.

An kama mutum uku da ƙwato wayoyin lantarki na sata 

Zan ci gaba da bada kuɗin hadaya kyauta — Gwamna Zulum 

Obasanjo na yunƙurin ɓata min suna don ɗan takararsa — Atiku

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe