Dirobobi biyar ’yan bindiga suka kashe mana a bana – Kwamared Abaji

Shugaban  Direbobin Tasi Masu Dogon Zango a Garejin Kawo a Jihar Kaduna, Kwamred Adamu Mohammed Abaji ya ce akalla direbobi biyar ’yan bindiga suka kashe a jihar a bana kadai. Ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Kaduna a wannan makon, yana mai cewa direbobin sun rasa rayukansu ne a […]

Dirobobi biyar ’yan bindiga suka kashe mana a bana – Kwamared Abaji
Dirobobi biyar ’yan bindiga suka kashe mana a bana – Kwamared Abaji

Shugaban  Direbobin Tasi Masu Dogon Zango a Garejin Kawo a Jihar Kaduna, Kwamred Adamu Mohammed Abaji ya ce akalla direbobi biyar ’yan bindiga suka kashe a jihar a bana kadai.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Kaduna a wannan makon, yana mai cewa direbobin sun rasa rayukansu ne a kan hanyoyin Birnin Gwari da Sabon Birni a Jihar Kaduna.

A cewarsa, rashin tsaro a titunan jihar ne babban kalubalen da ke fuskantar ’ya’yan kungiyar. “Gaskiya rashin tsaro ne babban matsalarmu a jihar nan musamman a kan batun garkuwa da mutane, wanda hakan ya sa har muka rasa direbobinmu biyar a yayin aikinsu. Kuma duk wannan abin fa ya faru ne a kan hanyar Birnin Gwari da Sabon Birni kadai. Saboda haka muna rokon a samar da tsaro a kan wadannan hanyoyi domin kare rayuwa da dukiyoyin jama’a,” inji shi.

Kwamared Abaji ya kuma bukaci gwamnati ta dauki mataki a kan masu bude tasoshin mota a bakin titi maimakon su rika zuwa gareji. Haka kuma ya bukaci a taimaka wajen samar musu da fitilu a garejin da za su taimaka wajen haskaka wajen musamman idan dare ya yi.