Diwanin Wakokin Shata: Sai Alasambarka

Sunan Littafi: Diwanin Wakokin Baka Juzu’i Na Uku: Matanonin Wasu Wakokin Alh. Dr. Mamman Shata Katsina Marubuci: Sa’idu Muhammad Gusau. Kamfanin Wallafa: Century Research & Publishing Ltd. Kano Shekarar Wallafa: 2018. Yawan Shafuka: 511 Farashi: Naira 3000 Mai Sharhi: Dokta Bukar Usman OON Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar rubuta Alsambarka ga […]

Diwanin Wakokin Shata: Sai Alasambarka


Sunan Littafi: Diwanin Wakokin Baka Juzu’i Na Uku:

Matanonin Wasu Wakokin Alh. Dr. Mamman

Shata Katsina

Marubuci: Sa’idu Muhammad Gusau.

Kamfanin Wallafa: Century Research & Publishing Ltd. Kano

Shekarar Wallafa: 2018.

Yawan Shafuka: 511

Farashi: Naira 3000

Mai Sharhi: Dokta Bukar Usman OON


Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar rubuta Alsambarka ga wannan Diwani da Shehun Malami, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya rubuta, musamman a kan wasu wakokin Dokta Mamman Lawal Shata Katsina; mashahuri a fagen wakokin baka na Hausa. Ina kuma gode wa marubucin da ya karrama ni, ya ba ni damar tofa albarkacin bakina a kan wannan gagarumin aiki da ya gudanar.

Kamar yadda sunan wannan diwanin ya nuna, wannan littafi shi ne juzu’i ko kundi na uku da Shehun Malami Gusau ya tattara na wakokin baka na Hausa. Idan ba a manta ba, juzu’i na daya da aka wallafa a shekara ta 2009, mai shafuka 516 yana kunshe ne da wakokin baka na Hausa guda 143. Sun hada da wakokin masarauta da na game-gari, wadanda suka shafi kowa da kowa, kama daga mutane ko dabbobi, gami da tsuntsaye, kwari da tsutsotsi daban-daban. Littafin ya kunshi mawaka da yawa. 

A bayanin da mawallafin ya yi a wancan diwani na daya, ya ce wakokin da littafin ya kunsa na share fage ne. Kodayake a baya ya wallafa littattafai da yawa a kan makada da mawakan Hausa, ya fadi haka ne kuwa domin sanin cewa akwai sauran wakokin baka na Hausa masu dimbin yawa da za a ci karo da su jefi-jefi, a kawunan mutane da kundayen bincike a makarantu daban-daban (Gusau 2009: shafi dbi). Wannan matsalalar kuwa ta faru ne tun asali saboda rashin mai da hankali a kan adana wakokin kamar yadda Farfesa Gusau ya yi a diwani-diwani da ya wallafa har uku kawo zuwa yanzu.

A kan haka ne kuma marubuci Farfesa Gusau bai tsaya ga diwani na daya ba, ya ci gaba da tattara wasu wakoki, aikin da ya kai shi ga rubuta diwani na biyu a shekara ta 2014. Shi wancan juzu’i mai shafuka 503, ya kunshi wakokin baka na Hausa guda 176, wadanda kamar diwani na daya, mawaka daban-daban ne suka rera.

A wannan karon, Shehun Malami Gusau ya samu karfin gwiwar tattara wakokin Dokta Mamman Shata kadai a wannan juzu’i na uku. A bisa bayanin da mawallafin ya bayar, wannan littafi mai kusan shafuka 509, da ya kunshi wakokin Dokta Mamman Shata guda 148, kadan ne daga cikin wakokinsa, domin kuwa Shata ya yi wakoki fiye da 10,000, kasancewar an samu bayanin cewa a lokacin da yake raye; yakan samar da wakoki kusan 200 a kowace shekara. Idan aka lura, yawancin wakokinsa ke nan suna nan warwatse, ana neman tattarawa. Duk da haka, ’yan kadan din wakokin Dokta Mamman Shata da wannan diwani ya kunsa, sun isa kuma ya zama wajibi ga duk wanda ya karanta ya yaba wa Dokta Mamman Shata kan irin nasarar da ya samu a fagen wakar baka ta Hausa; har da ya kai shi ga samun digirin yabo daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a 1988. 

An ce yabon gwani ya zama dole. Shi Dokta Mamman Shata, kamar yadda wani bangare na tarihinsa ya nuna, bai yi karatun boko ba. Hasali ma, makarantar Muhammadiyya da ya yi, bai yi karatu mai zurfi ba. Ya soma waka tun yana dan shekara 14.  Bai gaji waka ba kuma bai matsa wa ’ya’yansa su gaje shi ba a fagen waka. A lokacin da babban dansa Muhamman Lawan Shata ya fara waka ma, an samu bayanin da ya tabbatar da cewa marigayin hana shi ya yi, ya nuna masa cewa ya fi son ya yi karatun boko.

“Mai tambura na Bilkin Sambo” kamar yadda ake masa kirari, a bisa sanina, babu wani mahaluki da yake tsara masa wakokinsa kuma ba ya rubutawa kafin rerawa. A duk lokacin da ya nufi yin waka, takan zo masa kawai kamar saukar ruwa bisa horewar Allah. Dokta Shata, kafin mutuwarsa, bai adana kundin wakokinsa da kansa ba. Kuma bai mallaki kayan kida masu tsada ba, abin da kawai ke gare shi sai kalanguna da abin kara wa sauti amo na makirfo da sifika ko amsa-kuwwa.

Dama dai mawallafin ya bayyana kayan kade-kaden mawakan baka na kasar Hausa nau’i-nau’i ne kuma ba su da tsada. Hatta tafa hannuwa irin yadda ’yan mata masu wakokin dandali kan yi shi ma an dauke shi a wani tsari na kida, wanda kan kara wa wakokin armashi (Gusau 2014: juzu’i na biyu shafi dii).

Dokta Mamman Shata, wanda ya cika kusan shekara 80 kafin rasuwarsa a 1999, dan baiwa ne a fagen waka, wanda ya dogara ga basira da hazakar da Allah Ya ba shi wajen iya kaga wakoki masu ma’ana da nishadantarwa a kowane lokaci a kuma ko’ina. Baiwar Allah ke nan! Tunda a da can an dauke shi a matsayin makaskanci, mai tallar goro da alewa, har ya girma ya shahara a fagen waka, yana cin gashin kansa.

Ni kaina a yau da ke da shekara 75 a rayuwa, na san Dokta Mamman Shata a fagen waka tun ina yaro amma sau daya kawai na taba haduwa da shi a wani dakin taro a garin Bauchi. Na zauna kusa da shi a kan kujera. Bayan dan tadi kadan da muka yi, na taya shi murnar digirin yabo da ya samu. Allah da ikonSa, ya samu digirin a 1988 kuma ya rasu a 1999. Haduwata da shi, ta faru ne a tsakanin wadannan lokuta (1988-1999), domin kuwa ba zan iya tuna ranar ko watan da muka hadu da shi a Bauchin ba.

A kwana-kwanan nan, na karu da ilimi a kan fasahar Dokta Mamman Shata a fagen waka. Wannan ya faru ne lokacin da aka gayyace ni a matsayin Babban Bako Mai Jawabi, a wani taron kasa-da-kasa da aka shirya gabatarwa a Jami’ar Tahoua a Jamhuriyyar Nijar. Taron, wanda jami’ar ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar Pleasant Library and Book Club ta Katsina, an so a gunadar da shi a ranar 17 zuwa 20 na watan Augusta, 2017. Taron an shirya shi musamman saboda mahalarta su yi nazari a kan rayuwa da ayyukan marigayi Mamman Shata da wasu mashahuran mawaka na kasar Nijar. Allah da ikonSa, sai da aka kusa gama shiri sai wani dalili ya sanya aka daga taron, ana sauran ’yan makonni kadan kafin a yi.

Ina godiya da kokarin shirya wannan taro, kuma duk da ba a samu damar gudanar da shi ba, taron ya sanya ni na tsunduma cikin wasu ’yan binciken-binciken karin ilmi a kan wakokin Dokta Mamman Shata. Binciken ya kara mini ilimi a kan wasu wakokinsa da suka gabata a da can baya, wakokin sun kayatar da ni ainun. Wakokin kuwa su ne a kan wani sabani da ya faru tsakanin Dokta Mamman Shata da Ibrahim danmani Caji Bauchi. Wakoki tsakanin mawakan biyu sun samo asali ne sakamakon takaddamar da ta faru bisa bambancin ra’ayinsu a kan sha’anin aure da karuwanci. 

Da na soma bincike ne na samu bayani mai gamsarwa kuma na gaskiya daga wajen Shehun Malami Farfesa Gusau marubucin wannan diwani. A cikin kankanen lokaci ya ba ni cikakken bayani a kan tushen sabanin nan. Abin alfahari ne da na ga a cikin wannan diwani duka, wakokin da Dokta Mamman Shata ya yi a kan batun aure da karuwai sun fito a shafuka na 429 zuwa na 434 da takensu, wadanda suka hada da ‘Na Ga Jahilci Wurin Karuwai’ da ‘Ku Wa Allah Ku Bi Aure Mata’ da ‘Don Sallah da Salatil Fatih, Kai Don Allah Mata Ku Yi Aure.’ 

Littattafai guda 21 da Shehun Malami Farfesa Gusau ya wallafa daga 1991 zuwa shekara ta 2016, kusan rabi ya wallafa su ne game da makada da mawakan Hausa. Farfesa Gusau ya yi fice kwarai da gaske a wannan fannin matattara da ya dauki nauyin yi. Don haka babu shakka a yau har gobe, Farfesa Gusau da littattafansa za su taimaka kwarai ga dukan masu bincike da manazarta da dalibai su fahimci yadda mawakan suka tsara wakokinsu na baka na Hausa da kayan kade-kadensu da falsafofin da ke kunshe a cikinsu domin kyautata rayuwar ’yan Adam. A cewar Dokta Mamman Shata ‘Sai mutum ya sanka yake ma kida’ (Gusau: juzu’i na uku shafi 139). Wannan ya nuna ke nan, duk wadanda Dakta Maman Shata ya yi musu wakoki, ya dan yi kokarin sanin wani abu game da su.

Daga karshe, ina ba mawalafin wannan diwani shawara, cewa a nan gaba idan za a sake tattara muhimmin aiki irin wannan ko a sake masa fasali, to a hada da koda dan takaitaccen tarihi da hoto ko hotuna na mawakin. Ina ganin yin haka zai kara armashi ga diwanin nan da aka shirya a kan mashahurin mutum irin marigayi Alhaji Mamman Lawal Shata Katsina D.Litt., MON, ya cika cif.

Bukar Usman, Daktan Adabi (D.Litt.), OON

Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban kasa, Abuja Kuma Shugaban Kungiyar Manazarta Adabin Gargajiya ta Najeriya.

 

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya