Diyata ce ta nemi in yi lalata da ita – Wanda ya yi wa diyarsa ciki

‘Yan sanda a Jihar Legas sun kama wani mutum mai suna Taiwo Oyelabi mai shekara 50 a duniya da laifin dirka wa diyarsa ciki. Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Edgal Imohimi, a lokacin da yake gabatar da  mai lafin  a hedkwatar ’yan sandan jihar, ya bayyana wa manema labarai cewa sun samu rahoton ne tun […]

Diyata ce ta nemi in yi lalata da ita – Wanda ya yi wa diyarsa ciki

‘Yan sanda a Jihar Legas sun kama wani mutum mai suna Taiwo Oyelabi mai shekara 50 a duniya da laifin dirka wa diyarsa ciki.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Edgal Imohimi, a lokacin da yake gabatar da  mai lafin  a hedkwatar ’yan sandan jihar, ya bayyana wa manema labarai cewa sun samu rahoton ne tun a ranar 16 ga watan Afrilu..

Da yake bayanin yadda lamarin ya auku, Mista Taiwo ya ce, “Sau biyar kawai na yi lalata da diyata, kuma a cikin gidana ya faru. Ita ce ta nemi ni ta hanyar fara sumbata ta da rungume ni a lokacin da nake kwance a gado, sannan ta fito fili ta bukaci da in yi lalata da ita. Da farko na yi mamaki, amma daga baya sai na amince da bukatar ta.”

“Lallai ita ce fara nema, amma daga baya kuma na ci gaba da namanta,” inji shi.  

 “Wannan aikin shaidan ne, yanzu ga shi ban san yadda zan yi da dan ba. Na yi tunanin kashe kai na bisa wanna mummunar ta’adi da na aikata. Sau biyu ina neman halaka kai na, amma bai yiwu ba. 

“Wannan aikin shaidan ne, amma ina rokon Allah da ’yan uwana su yafe mani.

“Duk lamarin ya samo asali tun daga lokacin da muka rabu da matata, wadda ita ce uwar wannan yarinyar. Sai ta tafi da dukan ’ya’yana, amma daga baya sai ita wannan diyar tawa da dawo wajena da zama a shekarar 2017. Tun daga nan aka fara samun irin wannan matsalar.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce bayan sun gudanar da bincike, sai aka tabbatar da diyar  tana dauke da juna biyu na ubanta.  

Kwamishinan ’yan sandan ya ce da zarar sun kammala bincike za su tasa keyar Taiwo zuwa kotu.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana