Diyyar N100bn: Matatar Ɗangote ta janye ƙarar da ta maka NNPCL

Matatar Ɗangote na shirin janye ƙarar da ta shigar na neman diyyar Naira biliyan 100 daga hukumar kula da kasuwancin man fetur (NMDPRA) da NNPC

Diyyar N100bn: Matatar Ɗangote ta janye ƙarar da ta maka NNPCL

Kamfanin Matatar Man Ɗangote ta ce za ta janye ƙarar da ta shigar na neman diyyar Naira biliyan 100 daga hukumar kula da kasuwancin man fetur (NMDPRA) kan dambarwar shigo da man fetur Najeriya daga ƙasashen waje.

Matatar Ɗangote ta shigar ƙarar ne kan lasisin da hukumar ta bai wa kamfanin Matrix Petroleum Services na shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

Amma Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina, ya ce za su janye ƙarar kafin a koma kotun domin ci gaba da shari’ar a watan Janairu, 2025.

A lokacin zaman kotun, lauyan Matatar Ɗangote, George Ibrahim (SAN) ya shaida wa Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa ɓangarorin da ke shari’ar sun fara tattaunawa domin janye ƙarar da kuma sasantawa a wajen kotu.

Matatar ta shigar da kara ne a gaba kara ne kan lasisin shigo da tataccen mai da NMDPRA ta bai wa kamfanin Matrix Petroleum Services.

Manajan Daraktan Hulda da Gwmanti na matatar, Ahmed Hashem, ya ce hakan yana kawo cikas ga harkokin man da matatar take tacewa a cikin gida, kuma ya saɓa wa Dokar Man Fetur ta Nijeriya.