Diyyar sansanin Boko Haram da Gwamnatin Tarayya ta ba mu bai isa ba — Gwamnatin Gombe
Gwamnatin ta ce kamata ya yi a biya jihar kuɗin da suka fi wanda aka ba ta a yanzu.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya koka cewa Gwamnatin Tarayya ba ta biya jiharsa diyya yadda ya kamata ba, bayan ta mayar da sansanin masu yi ƙasa hidima (NYSC) na Malam-Sidi wajen gyaran tsofaffin ’yan Boko Haram.
Gwamnan, ya bayyana haka ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, inda ya ce jihar ta samu Naira biliyan 1.4 kacal.
- Gobara ta ƙone shaguna 22 a kasuwar shanu a Kwara
- Kotu ta ba da belin wadanda ake zargi da kashe matafiya daurin aure a Mangu
Ya ce kamata ya yi a biya jihar sama da Naira biliyan biyar domin gina sabon sansanin NYSC.
Farfesa Njodi, ya ƙara da cewa ɗaliban makarantar sakandaren ‘yan mata ta Amada sun rasa matsuguni, bayan da aka mayar da wajen sansanin wucin gadi na NYSC.
A nasa jawabin, shugaban Operation Safe Corridor, Rear Admiral Suleiman Abdullahi, ya ce za su ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin jihar da al’umma domin tabbatar da shirin gyara tsofaffin ’yan Boko Haram da suka miƙa wuya ya yi nasara.