DND zai ba al’umma damar daina karbar sakon da ba sa bukata – NCC
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa (NCC) ta ce ta fito da wata lamba da ake kira DND (Do Not Disturb) mai dauke da lambar 2442 da za ta rika ba mutum ko wata hukuma damar daina karbar duk wani sakon da ba ya bukata daga kamfanonin wayoyin sadarwa da suke mu’amala da su. […]

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa (NCC) ta ce ta fito da wata lamba da ake kira DND (Do Not Disturb) mai dauke da lambar 2442 da za ta rika ba mutum ko wata hukuma damar daina karbar duk wani sakon da ba ya bukata daga kamfanonin wayoyin sadarwa da suke mu’amala da su.
Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umaru dambatta ne ya sanar da haka a wajen taro karo na 82 na masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa da ya gudana a Abuja. Ya ce hukumarsa ta bullo da wannan tsari ne don ba al’umma zabin irin sakonnin da yakamata su rika gani daga kamfanonin sadarwa da suke yin hulda da su a fadin kasar nan.
Farfesan ya kara da cewa tsarin bAS yana da matukar muhimmanci a harkar sadarwa, inda tsari ne da ke ba mutum damar ya rika tantance irin sakonnin da zai rika samu daga wajen kamfanonin sadarwa idan ya yi amfani da tsarin lambobin 2442.
Ya ce tsarin zai rika ba kamfanoni damar su rika aika muhimman sako ga kwastomominsu, wadanda kwastomomin suka zaba don a rika aika musu, walau ta wayoyin sadarwarsu ko ta takardu ko mujallu ko ta wadansu hanyoyin sadarwa da hakan zai sa su rika tallata hajojinsu cikin sauki. Sannan muhimmancin yin amfani da wannan tsari zai sa kamfanonin su rage aika sakonnin da kwastomominsu ba sa bukata.
“Wannan ta sa muka fito da tsarin da zai rika ba kamfanonin sadarwa aika sakonni zuwa kwastomomi cikin sauki da kuma cikin tsari a daya dangaren kuma zai kare kwastomomi daga aika musu sakonnin da ba sa bukata”, inji Farfesa dambatta.
Ya ce Hukumar NCC ce ke da alhalin kula da kamfanonin sadarwa ta hanyar ba su lasisin da suke gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba, sannan a daya bangaren kuma hukumar ta samar da tsarin DND ne don ba al’umma damar amfani da tsarin wajen hana kamfanonin aika musu duk sakon da ba sa bukata. Kenan kwastomomin suna da zabi a irin sakonnin da kamfanonin sadarwar za su rika aika musu ko ma su dakile su wajen aika musu kowane irin sako.
“A kan haka ne Hukumar take shirya tarurruka don fadakar da al’umma muhimmancin rungumar tsarin DND da hakan zai ba su zabin amincewa ko rashin amincewa game da aika musu kowane irin sako daga kamfanonin sadarwar da suke hulda da su”.
A taron karo na 82 da aka yi masa taken: balue Added Serbice (Inganta Harkar Sadarwa), Farfesa dambatta ya nanata cewa Hukumarsa za ta ci gaba da bullo da hanyoyin da za su rika kare ma’abuta amfani da layin sadarwa da suka hada da ma’aikatan gwamnati da ’yan kasuwa da maza da mata da kungiyoyin mata da dalibai da sauransu.
“Ina tabbatar muku da cewa, Hukumar NCC ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare hakkin kwastomomin da ke amfanin da layukan sadarwa a kasar nan musamman ganin cewa da bazarsu kamfanonin sadarwa ke yin rawa”.
A nasa jawabin Daraktan hulda da jama’a na Hukumar NCC Alhaji Abdullahi Maikano ya ce hukumar tana gudanar da taron da ke hada masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa TCP ne don a rika lalubo matsalolin da ke damun al’umma da na kamfanonin sadarwa don a gudu tare kuma a tsira tare.
Alhaji Maikano ya kara da cewa gudanar da irin wannan taro yana da matukar muhimmanci don yana bayar da kafar samar da muhimman bayanai da bayar da shawarwarin da za su sanya a rika samun bunkasa a harkar sadarwa a kasar nan”.
“A kan haka ne muka yi wa taken taronmu na bana “Inganta Harkar Sadarwa” don a ba kamfanonin sadarwa da al’umma damar lalubo hanyoyin da zai sa a inganta yanayin sadarwa a kasar nan”.