‘Dodanni’ sun farmaki coci a Filato, sun zane Fasto da masu ibada
An kai harin ne ana tsaka da ibada a cocin
Mambobin cocin bayan harin
Wasu dodanni a kauyen Shikal da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato sun kai farmaki wata majami’a ranar Lahadi, inda suka lakada wa Fasto da masu ibada dukan tsiya.
An dai kai farmakin ne ranar Lahadi lokacin da mutane ke tsaka da ibada a cocin.
- ‘Kwanan nan za a yi dokar da za ta haramta cin ganda a Najeriya’
- Bello Turji ya sake tsallake rijiya da baya a harin sojojin sama
Baya ga dukan masu ibada, dodannin sun kuma tarwatsa zaman cocin tare da lalata kayan kade-kaden da ke cikinta.
Wata majiya ta ce ba a san dai mace ce manufar dodannin ba, amma mambobin cocin ba su mayar da martani ba.
Ya kuma ce matakin bai jawo wata hatsaniya ba a kauyen, kodayake har yanzu shugabannin kauyen na kokarin lalubo ainihin musabbabin harin domin a magance shi a gaba.
Sai dai har zuwa yanzu Rundunar ’Yan Sanda ta jihar ba ta magantu ba a kan lamarin.