Dodo ya kai hari, ya kashe mutum a masallaci

Mabiyan dodo sun bindige mutum daya, sun jikkata wasu da dama a masallaci.

Dodo ya kai hari, ya kashe mutum a masallaci

Masallaci da aka kai wa masu ibada hari. (Hoto: BBC).

An bindige mutum daya tare da jikkata wasu da dama a yayin da suke tsaka da ibada a wani masallaci a garin Osogbo, Jihar Osun.

Mutanen na tsaka da gudanar da addu’o’i na musamman a karkashin wata rumfa a masallacin ne wani dodo da mabiyansa suka far musu a ranar Lahadi.

An kai wa masu ibadar hari a masallacin ne a yayin da masu dodon suka biya ta harabar Oluode Aranyin, kusa da masallacin.

Maharan sun lalata tagogi da kofofin masallacin a harin da suka kashe wani mutum mai suna Moshood Salawudeen.

Babban Limamin Masallacin, Alhaji Quoseem Yunus, ya ce babu wani sabani a baya tsakanin masu ibadar da masu dodon.

Limamin ya ce da farko sai da masu dodon suka ratsa yankin ba tare da sun far wa masu ibadar ba.

Ya ce bayan sun ci gaba da ibadar tasu a harabar masallacin ne dodon da mabiyansa suka sake dawowa suka far musu.

Wadanda suka samu raunuka a yanzu haka suna kwance a asibiti  a garin Osogbo, yayin da aka ajiye gawar mamacin a dakin ajiyar gawarwaki.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Osun, Yemisi Opalola, kuma ba a same ta ba a lokacin hada wannan rahoton.

Zaɓen Edo: INEC ta dakatar da tattara sakamako

Zaɓen Edo: Magoya bayan PDP sun fara zanga-zanga 

Kwalara ta yi ajalin mutum 12 a Adamawa

Tsadar Rayuwa: Matar Tinubu ta raba wa ɗalibai littafan rubutu a Nasawara