Dodorido
Assalamu alikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. A madadin shagabannin wannan makaranta na riko, muna ban hakuri na rashin ganin sakonnin ’yan makaranta a akai-akai a wannan Amintacciyarr Jaridar da ake bugawa a kasar Haurobiya da ja gabanta Farfesa DODO uban DOODANNI, kuma ina kira ga Aliyu da Aliya ina danladi da Ladiya; ina Gambo […]
Assalamu alikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. A madadin shagabannin wannan makaranta na riko, muna ban hakuri na rashin ganin sakonnin ’yan makaranta a akai-akai a wannan Amintacciyarr Jaridar da ake bugawa a kasar Haurobiya da ja gabanta Farfesa DODO uban DOODANNI, kuma ina kira ga Aliyu da Aliya ina danladi da Ladiya; ina Gambo da Gamboliya ina Hali da Halima ina Jamila da Jamilu ina Khalis da Khalisa ina danlami da Lami, ina Malam da Malama ina Nafi da Nafi’u ina Olu da Oluwa yaran baba, ina Patric da Patricia ina kinki da kei ’yan garin Jani-inatili ina Rabi’u da Rabi’a ina Sani da Saniyya ina Talatu da Talatuwa ina Balan-tine da Tineruwa ranar gwangwajewa ina Walid da Walida ina Yahaya da Yahanasu hada da Zakiyyu da Zakiyya kai har ma wanda ban kwararo sunansa ba, don na bi lungu-lungu mararraba-marraba don raba goron hakuri. Sannan sako-sako don isar da sakonku a kara na-damo a kan abin da ya shude. Kuma kofa a bude take ga dalibai da masu sha’awar wannan makaranta tamu mai albarka ta DODORIDO,
A karshe nake rokon Mai-duka Ya kara wa Sheihin malami ingancin uwar jiki ba tare da jan jiki ba don gudanar da aiki lafiya.
Daga: Jami’in Hulda da Jama’a na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu 08034332200
Ta’aziyya
Assalamu alikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. A madadin daliban wannan makaranta tamu mai tarin albarka ta Dodorido reshen Jihar Tumbin-giwa, muna mika ta’aziyyar yayanmu, malaminmu, kuma ubanmu Khalifa na Kwanar Gaban-gari da ke cikin birnin Dabo Kuma yaya ga Malam Usman. Mai-duka Ya kai rahama ga makwancinsa. Al’umma mu ce amin baki sili, bayan Sallah da salati.
Illar tallace-tallacen ‘yan dugwi-dugwi
’Yan dugwi-dugwi muna ganin cewa tallar da suke yi talalar talauci ne ai ta talau-talau ce yake kawo shi saboda neman yadda za a tsira da rayuwa. Wasu daga cikinsu ko makarkata ba sa samun damar zuwa sai sun yi ta karkarwa saboda yanayin da suke ciki tare da iyayensu.
Wasu ’yan dugwi-dugwin kuma suna zuwa koyon watsatstsakene amma da zarar sun dawo za su dauki kayan talla don samo yadda za su biya kudin makaranta da kudin zuwa Islamiyya da sauransu. Kadan daga cikin illolin tallace- tallacen ’yan dugwi-dugwi su ne;
’Yan dugwi-dugwi sukan yi mu’amala da jama’a wajen yin tallace-tallacensu ciki har da lalatattu da abokai na banza su koya musu shaye-shaye da romo irin na kayan bokan Turai da kara wa duniya hazo da yawon ta zubar, saboda ganin iyaye sun kasa kula ko unguwanni, har su ma suke jan makwabtansu wajen yada wannan fasadi, ta hanyar dan ba su da damin Hauro ko za su yi biki ko wani bidiri kai tsaye za su nemi masu amfani da su, don biyan bukatarsu. Kuma wai har ake yi musu kallon cewa su abin sha’awa ne a cikin kawayensu mata. Muna rokon Mai-duka Ya yaye mana wannan masifar. Iyaye kuma su ji tsoron Mai-duka a cikin kiwon da Ya ba su ta ’ya’yansu. Su kuwa masu lalata ’ya’yan mutane, muna jan hankalinsu da su ji tsoron Mai-duka su daina. EHEE
Daga: Jami’in Hulda da Jama’a na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu 08034332200.
Tambaya ga Malam
Barka da warhaka, wata rana ina karanta jaridar Aminiya sai na yi karo da wasu kalmomi wadanda na kasa fahimtar ma’anarsu duk da dai cewa, ni ba kwararre ba ne a Hausa amma, ina roko tare da kaskantar da kai da a fassara min su. Ga kalmomin kamar haka:- kurtu, karamin lauje, madambaci, sili da babban lauje. Zan kasance mai mutukar farin ciki idan an amsa min wadannan tambayoyi.
Yusuf Isah, Jos. Bawan Allah [email protected]
An yi wa Saurayin-Kirinki ruwan tsingaro
Sallama irin ta masu duban alkibla don kadaita Mahalicci. Ina fatan Malam Dodo da sauran ’yan makaranta sun sallata cikin managarciyar uwar jiki. Da alama dai kwalliya na shirin biyan kud’in sabulu a wannan mulaka’u na Damo-da -Kura-da-diya.
Domin idan ban sanya takalmin Malam Mantau ba, a makonni da suka arce mai gidanmu Malam Dodo ya yi wa Saurayin Kirinki wa’azi da nasiha a kan ya yi kokarin zama saurayin kirki. Sai dai kash! Abin da wuya wai gurguwa da auren nesa. Domin jifan Azazilu da Haurobiyawan garin da kogin ke kwarara suka yi wa Saurayin Kirinki a filin gundumemiyar Sallar Baba-Idi ta bana, ya nuna yadda Saurayin-Kirinki ya rigaya ya yi barin da ba zai iya kwashewa ba. Wannan ya nuna cewa, ya rigaya ya baro kari tun ran tubani, domin zai yi wuya Haurobiyawan da suka jajirce wurin tabbatar da Burin-huriyya su rungume hannu wani bara-gurbi ya kassara kyakkyawan burin ganin an gyara Haurobiya, har ta zarce Italiya da Romaniya.. Gani ga wane dai ance ya ishi wane tsoron Allah.
Daga Ashiru dan’azumi Gwarzo [email protected] [email protected]/07036589807
Turakun ma’aurata
’Yan makarantarmu za a turke ni da wata salihar mata, ’yar Santalusiya, kuma ’yar Taiwan a garin Girkin Jihar Jijjiga -ciyawa. Za mu yi ruguntsumin dabdalar bikinmu ranar babban lauje ga watan Dashen-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje.
Daga dahiru Abubakar MMR. Ja-gaban daliban dodorido na Jihar Jijjiga-ciyawa 07039267379.