Dogara ga Ubangiji 2

Karin Magana 3:5-7, “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai. Sam, kada ka yarda ka dauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, […]

Dogara ga Ubangiji 2

Karin Magana 3:5-7, “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai. Sam, kada ka yarda ka dauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.”

Muna yi wa Ubangiji godiya domin kaunarSa da alheranSa zuwa gare mu har Ya kawo mu ga rana ta yau.

Makon da ya shige mun ga yadda mutane ke dogara ga dukiya da matsayi da kuma iliminsu cikin rayuwarsu ta yau da kullum, ba sa tunanin dogara ga ikon Ubangiji Allah ba, a ganinsu mallakarsu kan kare su daga bala’i da kuma kara musu tsawon kwanaki a duniya. 

A wannan mako kuma za mu ga yadda wadansu mutane kan kasa tuna cewa Ubangiji Allah ne madogaransu a duk lokutan da suke cikin rashi ko rashin lafiya da makamantansu. Sau da dama za ka ga wadansu mutane na sa kansu cikin wasu irin halaye, misali, fashi da makami da sata da zamba da karuwanci har ma yakan kai ga kisan kai cewa su ne hanyar tsira daga cikin tsananin da suka samu kansu a ciki. 

Bari mu sake dubawa cikin karatunmu na makon jiya, inda Yesu Almasihu ke magana kan irin wadannan halaye da mutane ke gani babu wata hanya in ba irin wadannan halayen da muka ambata ba. Littafin Matiyu 6:26-34, “Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na sama Yana ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba? Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko da taki ga tsawon rayuwarsa? To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin daji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baki, duk da haka ina gaya muku, ko Sulaimanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na dayansu ba. To, ga shi, Allah Yana kawata tsirrran daji ma haka, wadanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a wuta, balle ku? Ya ku masu karancin ban-gaskiya! Don haka kada ku damu, cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin wadannana bubuwa, Ubanku na sama kuwa Ya san kuna bukatarsu duka. Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukan wadannan abubuwa. Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. dawainiyar yau ma ta ishi wahala.” 

Abu mafi muhimmanci idan ka samu kanka cikin irin wannan hali, shi ne sai ka bidi nufin Ubangiji Allah ta wurin addu’a, Shi kuwa Mai adalci ne zai ji addu’arka idan ka yi ta da ban-gakiya ka kuma dogara cewa Shi Ubangiji Allah Mahaliccinka Ya fi kowa sanin komai game da yanayin da kake ciki zai kuma biya maka bukata. Mu guji irin wadannan halaye, har ma zuwa wurin bokaye domin tsafin neman biyan bukata, ka tambayi kanka mana dan uwa, shi boka ya fi Ubangiji Allanka girma da iko ne? To me zai hana ka zuwa wurin wanda ba zai tambaye ka bakar kaza ko kan mutum dan uwanka ko kudi ba domin biya maka bukata? Addu’a da ban-gaskiya kadai Ubangiji ke bukata a gare ka. 

Iblis ne ke rudin mutane, ba ya ba da kyauta haka kawai, muradinsa ya kai mutum ga hallaka na har abada. A koyaushe bari tunaninmu ya zama cikin tafarkin Ubangiji, Shi kuma zai nuna mana hanyar da take daidai. Ubangiji Allah ne Ya hallicci sama da kasa da duk abin da ke cikinsu, Shi Ya hallicci kowa da komai, mai rai da mara rai, mutane da dabbobi, na teku da masu tafiya a kasa, ittatuwa da kwari… kuma Shi Yake ciyar da kowa da komai (kamar yadda muka karanta), ka dubi girma da ikon Ubangiji mana, sai ya zamanto ba itace ko dabba ba amma kai mutum da Ya halitta cikin ni’imarSa, Ya darajanta bisa duk halittunSa, sai ya zamana cewa‘mutum’ ne ya kasa sani da kuma dogara ga Ubangiji Ya biya masa bukatunsa,  abin tausayi. 

Bari mu bar halinmu na dogara ga mallakarmu da matsayi da iliminmu, ko talauci da rashinmu, mu dogara ga Ubangiji Allah Shi kuma ba zai yashe mu ba. 

Mu komo ga Ubangiji tun muna raye.

Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ganewa cikin tafarkinSa. Amin.