Dogara ya amince ya sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai

Shugaban Majalisar Wakilai, Honarabul Yakubu Dogara ya amince ya sake takarar kujerar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Fatawa Balewa a Majalisar Wakilai. Dokara ya bayyana hakan ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Hassan Turaki ya aike wa Aminiya. Dogara ya bayyana wa dumbin magoya bayansa da suka zo gidansa na Abuja […]

Dogara ya amince ya sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai
Dogara ya amince ya sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai

Shugaban Majalisar Wakilai, Honarabul Yakubu Dogara ya amince ya sake takarar kujerar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Fatawa Balewa a Majalisar Wakilai.

Dokara ya bayyana hakan ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Hassan Turaki ya aike wa Aminiya.

Dogara ya bayyana wa dumbin magoya bayansa da suka zo gidansa na Abuja ne a ranar Talata domin nuna goyon bayansu gare shi, inda ya ce ya amince ya amsa kiransu domin sake wakiltarsu tunda sun nuna suna son haka.

“Na amince zan sake tsayawa takara domin wakiltar ku. Ban yi tsammanin zan wayi gari in ganku ba yau, amma bisa yadda kuka nuna min irin wannan soyayya, zan sake tsayawa kuma zan zo har gida mu sake haduwa inda zan tabbatar da aniyata.

“Wasu sun ce wai za su mana ritaya a siyasa, amma muna shaida musu cewa Allah kadai ne yake da wannan ikon, sai kuma masu zabe.”

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa