Dogara ya tallafa wa ’yan kasuwa da jari

daruruwan ’yan kasuwane suka amfana da tallafin karin jari a lokacin bikin hahuwar cika shekaru hamsin da Shugaban Majalisar Wakilai ta tarayya yayi a mazabarsa na Dass , Tafawa Balewa da Bogoro da ke cikin JIhar Bauchi. Al’amarin ya zo wa ‘yan kasuwa da al’ummar yankin tamkar a mafarki domin ba su zaci za a […]

Dogara ya tallafa wa ’yan kasuwa da jari

daruruwan ’yan kasuwane suka amfana da tallafin karin jari a lokacin bikin hahuwar cika shekaru hamsin da Shugaban Majalisar Wakilai ta tarayya yayi a mazabarsa na Dass , Tafawa Balewa da Bogoro da ke cikin JIhar Bauchi.

Al’amarin ya zo wa ‘yan kasuwa da al’ummar yankin tamkar a mafarki domin ba su zaci za a ba su wadannan miliyoyin Naira ba a wannan lokaci amma sai ga shi Shugaban Majalisar ya sa an ba da horo ga mata da matasa, inda aka koya musu sana’a, kuma ya ba su jari, sannan ya bi kasuwanni da kansa yana rarraba kudi ga ’yan kasuwa don su kara jari.

dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Misau da Dambam, Mallam Ahmed Yerima shi ya fara magana a wajen horon da aka bai wa mata da matasa domin karfafa jarinsu da nufin bunkasa kasuwancinsu.

Ahmed Yerima ya shaida wa kimanin mutane 526 maza da mata da suka fito daga yankunan kananan hukumomi na Jihar Bauchi suka samu tallafi na Naira miliyan 156 karkashin shirin ba da tallafi don yakar talauci da shugaban majalisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara ya bayar, cewa an ba su wannan talafi ne domin su yi sana’a saboda Allah, kuma ba don siyasa ba.

Yerima ya ce manufar gudanar da wannan shiri na koyar da sana’a da bayar da  tallafi an yi shi ne domin a koya wa mahalartan yadda za su zamo masu sana’a na kashin kansu, kuma a lokacin bayar da horon an horar da su yadda za su sarrafa abincin da ake nomawa, kamar wake da shinkafa su sanya su cikin kwatarniya ko jaka mai tsafta domin su sayar su samu riba.

Shugaban majalisar, wanda da kansa ya bayar da cekin kudin Naira 100 ga kowane daya daga cikin wadanda suka samu horon, don ya je ya yi irin sana’ar da ya koya, ya kuma mika takardar shaidar samun horon a dakin taro na jami’ar jeka kadawo na kasa, wato “National Open Unibersity”  dake Bogoro.

Chekin kudin dai an makalashine a jikin takardar shaidar samun horon wanda ke dauke da sunan bankin da mutum zaije domin ya karbi kudinsa.

Bayan da aka gama mika chekin sai wasu daga cikin mahalartan suka gwada irin basirar da suka koya a gaban kakakin majalisar da kuma sauran manyan bakin dake wajen

Da take jawabin godiya a madadin wanda suka samu tallafin hajiya uwaliya Inuwa wanda tafito daga karamar hukumar dass,Tayi alkawarin yin amfani da irin sana’ar da suka koya domin kawar da talauci a cikin iyalansu dakuma yankunansu ,Sannan tayi godiya ga kakakin majalisar wakilai ta tarayya Right Honourable Yakubu Dogara saboda kishin daya nuna harya basu dama na yakar talauci.

Dayake jawabi a wajen taron kakakin majalisar wakilai ta tarayya Right Honourable Yakubu Dogara yace anshirya wannan shiri ne a matsayin kokarinsa na rage talauci tun daga karkara,yace ba dimokradiyyar da da zatayi nasa idan mutane suna cikin talauci.

Dogara yace yan uwa da abokansa sun tara masa kudi fiye da naira miliyan 300 na gudumawar da aka tara a wajen wani wsan kwallon kafa da kuma kaddamar da littafi na bikin cikar kakakin shekara 50 da nufin tallafa way an gudun hijira. 

Dogara yace dukkan abunda suka faru nasara ne na al’ummar wannan mazaba na Dass,Tafawa Balewa da Bogoro domin al’ummar mazabar ne suka tara kudi domuin su yaki talauci su kuma tallafa way an gudun hijira.

Bayan naira miliyan 300 da aka tara ina saran cewa za’a samu kari domin mutane da yawa suna zuwa suna cewa zasu bada gudumawa,yace wannan nasara namune gabadaya mu yan wannan mazaba domin da baku goyi baya kun tallafa mini ba baza’a samu wannan nasara ba,Da yake sake gode musu na daman da suka bashi suka sake zabanshi har akasamu wannan nasara. 

Dogara ya basu tabbacin cewa zaiyi kokari yaga ya tallafa wa kowa da kowa harda wanda basu zabeshi ba domin shi baya bambamci,Yace manufarsa shine yataimaki al’ummar da suke cikin talauci domin su fita daga cikin talauci sukai har arzikin da zasu kai a rayuwarsu, Sai ya rokesu da suyi amfani da wannan kyakykyawar kudin da aka basu suyi sana’ar da zai taimakesu da iyalansu

Kakakin majalisar yace wannan kudi bana siyasa bane don ba siyasa mukeyi anan ba muna kokari ne mu warware matsalolin da sukayi dabaibayi wa cigaban kasar mu, don nasha fada talauci shine babban abunda yake barazana wa dimokradiyyar mu, haryan kawai da zamu warwareshi shine mu maganceshi tun daga karkara saboda haka dolene dimokradiyya yaranka tafiya da cigaba, munzo nan don yakin neman zabe bane ba kuma munzo don mu bada horo bane munzo ne don musa kudin jari a hannunku tare da fatan zakuyi amfani dashi bazaku barshi ya lalace ba.

Dogara ya kuma yi wani abu na ba sabon ba inda yatallafawa daruruwan Yan kasuwa da dan karamin jari dazasu kara akan wanda suke dashi da nufin bunkasa harkokin kasuwancinsu.

Kakakin Majalisar ya ziyarci kasuwanni guda biyar dakuma kauyuka ajihar Bauchi inda ya gana da yankasuwa kuma ya basu tallafin kudade domin su bunkasa sana’arsu.

Dogara yabi Yan kasuwar shago shago da tebur tebur dama masu talla dukkan su yayi musu gaisuwa kuma ya tallafa musu da Karin jari.

Kakakin a lokacin da ya ziyarci kasuwannin yana tare da Matarsa Gimbiya Dogara da kuma dan majalisar dake wakiltan mazabar Misau Dambam Mallam Ahmed Yerima.

Daga cikin kauyukan da yaje kasuwannin su sun hada da kauyukan Burgel, Zwall, Kagadaman Dass, Mararraban Liman Katagum,da kuma Ka dage akan  hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa.

Mallam Adamu Dan Ningi dake sayar da nama akasuwar Mararraban Liman Katagum ya shaidawa Wakilin Aminiya cewa lokacin da kakakin majalisar wakilai ta tarayya ya iso kan rumfarsa ya tsaya inda yake sai da tumaki ya dubi tinkiyarsa fata rage ya tambayeshi kudinta yace kudinta Naira dubu 20 sai ya dauki Naira dubu 20 ya bani, sai ya dauki Naira dubu 20 ya bani yace in je in kara jari. Zanje insayi wata tunkiyar da ita shi mutumne mai taimakon jama’a ba tare da nuna bambanci b azan iya masa shaida akoina.

Shekaruna 37 kakakin majalisa ya bani kudi domin in bunkasa sana’ata tun da nake ban taba ganin zababbenshugaba a kasuwa yana bin shago shago teburi teburi ba sai yau danaga Dogara,

Abdullahi Shuwa yace Dogara yazo shagona ya kuma bani kudi na yarda da batunnan da ake cewa in kana da hakuri alherin Dogara ya yawaita zai zo wajenka da nayi hakuri gashi yau nima na karba.

Wani Dan bumburutu Sani asadi yace da Jarka biyu na fetur yake iya dauka amma yanzu zai iya daukan Jarka hudu daga Tallafin dubu goma daya samu a hannun Dogara.

Har ma wadanda basu samu ko kwabo ba sun yabawa kakakin majalisar yanda yazo ya badsa tasllafin da hannun sa ba sako ba, suma sunyi alkawarin yin kokari sukafa tebbur ko su sami shago domin watarana in yazo ta kansu suma su samu rabonsu.

 

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50